Synopsis
Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.
Episodes
-
Barazanar da mamayar ƴan China ke yi ga kasuwanci a sassan Najeriya
02/04/2025 Duration: 10minShirin Kasuwa A Kai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya yi dubi ne kan halin da fannin kasuwanci ke ciki a Najeriya sakamakon barazana ko ƙoƙarin mamaya da ƴan ƙasar China ke yi, wanda aka tabbatar da irin illar da ayyukansu ke haifarwa ga ƴan kasuwa da kuma tattalin arziƙin ƙasar. Ba sabon abu bane yadda ake samun ƴan ƙasar China da ke aikata abubuwan rashin ɗa'a kama daga ɓangaren haƙar ma'adai ba bisa ƙa'ida ba, yin kutse ga ƴan kasuwa, zamba cikin aminci a intanet da sauransu.Sai dai ana zargin har izuwa yanzu, babu wani tsatsauran mataki na azo a gani da gwamnatin ƙasar ta ɗauka wurin kawo ƙarshen irin waɗannan laifuffukan da ake samun ƴan ƙasar na yi a Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
-
Ƙananan kamfanoni na taka rawa wajen bunkasa tattalin arzikin yankin Sahel
26/03/2025 Duration: 10minShirin Kasuwa akai miki dole na wanan makon tareda Ahmed Abba ya yada zango ne jihar Maradi dake jamhuriyar Nijar, inda ya mayar da hankali kan rawar da kannan kamfanoni ke takawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar dake yankin Sahel. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......
-
Gwamnatin jihar Neja a Najeriya ta janye haraji kan ƙananan ƴan kasuwa da masu talla
12/03/2025 Duration: 09minShirin KASUWA AKAI MIKI DOLE na wanan makon ya maida hankali ne kan matakin da gwamnatin jihar Neja ta ɗauka na janye haraji kan ƙananan ƴan kasuwa da masu talla a faɗin jihar, a wani mataki na bunƙasa ƙananan ƴan kasuwa tare da samar wa da al'umma sauƙi a jihar. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......