Synopsis
Kawo aladu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jamaa masu aladu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Episodes
-
Yadda al'ummar ƙasar Hausa suka rungumi al'adar shaƙe a matsayin magani
04/02/2025 Duration: 10minShirin Al’adunmu na gado na yau, ya yi duba ne kan al’adar shaƙe a ƙasar hausa da wasu kan yi a matsayin al’ada da kuma magani. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
-
Ƴan China da ke Najeriya sun gudanar da bikin sabuwar shekararsu
28/01/2025 Duration: 09minShirin Al’adun mu na gado na wannan makon ya mayar da hankali ne ga bukuwan sabuwwar shekara na ƴan ƙasar China, bukukuwan da aka gudanar a sassa daban daban na duniyar. A Najeriya, ƴan China ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da wannan biki a biranen Abuja da kuma Lagas, wanda ya samu halarta jama’a baki daga ciki da waje. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
-
Yadda al'adar shaɗi ko kuma Charo ke gudana tsakanin al'ummar fulani a baya
21/01/2025 Duration: 09minShirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ke kan al'adar shaɗi ko kuma Charo na sahun manyan al'adun ƙabilar fulani a ƙasashen Afrika ta yadda har sai wanda ya iya karɓaɓɓen shaɗi ke iya samun matar aure, yayinda a wasu lokutan ake gudanar da wannan al'adu a shagulgula don nishaɗi kuma jajirtacce shi ne jarumi.
-
Yadda Hausawa ke ƙoƙarin yin watsi da al'adar amfani da kwarya
17/12/2024 Duration: 09minShirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa ke ƙoƙarin mancewa da al'adar amfani da kwarya, wacce ke cikin daɗaɗɗun kayan amfanin gida na Malam Bahaushe. To sai dai duk da irin tasirin Kwarya a cikin al’ummar ta Hausawa, sannu a hankalin wannan al’ada tana neman gushewa a tsakanin al’ummar ta Hausawa har ma da Fulani da suka rungumi al’adar daga baya. Masu harkar sayar da ƙore a yankin Arewacin Nigeria, na kokawa sosai kan rashin garawar sana’ar tasu sakamakon yadda Hausawa da Fulani suka rage amfani da Kwarya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........