Lafiya Jari Ce

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 4:00:34
  • More information

Informações:

Synopsis

Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.

Episodes

  • Ƙuncin rayuwa na jefa ɗimbin ƴan Najeriya cikin tsananin damuwa - Rahoto

    28/10/2024 Duration: 09min

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan matsalar damuwa mai dankwafarwa ko tsananin damuwa da ake kira Depression, cutar da ake ganin ta’azzararta a baya-bayan nan tsakanin ƙasashe masu tasowa musamman waɗanda ke fama da matsi ko kuma ƙuncin rayuwa. Wasu bayanan ƙwararru yayin bikin ranar lafiyar ƙwaƙwalwa da ya gudana a farkon watan nan, ya nuna yadda matsi da ƙunchin rayuwa ya jefa miliyoyin ƴan Najeriya a tsananin damuwar ko kuma damuwa mai dankwafarwa, matsalar da likitoci suka yi gargaɗin cewa ka iya kaiwa ga taɓin ƙwaƙwalwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu........

  • Yadda mutane ke kauracewa yin gwaje-gwajen lafiya na wajibi

    21/10/2024 Duration: 09min

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon yayi duba ne kan ƙalubalen da fannin lafiya ke fuskanta na yadda ake gani a halin yanzu jama’a ke tsoro ko kuma kaucewa gwaje-gwajen lafiya ciki kuwa da har da wajibi da suka ƙunshi hawajini da nau’in jini ko kuma rukuninsa duk kuwa da muhimmancin hakan ga lafiyarsu. A baya-bayan nan bincike ya gano yadda jama’a kan kaucewa yin gwaje-gwaje kama daga na wajibi ko kuma a lokacin kamuwa da cutuka, walau ko saboda tsoron gano wasu nau’in cutuka da ke tare da su ko kuma wani dalili na daban.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu......

  • Illar shan magani ba tare da shawarar masana kiwon lafiya ba

    14/10/2024 Duration: 09min

    Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne game da matsalar shaye-shayen magunguna ba bisa ka'ida ko kuma shawarwarin masana kiwon kiwon lafiya ba, wadda hakan ke haifar da matsaloli da dama a jikin dan'adam. 14/10/2024

  • Illar da hayaƙin taba sigari ke da shi ga lafiyar al'umma

    07/10/2024 Duration: 10min

    Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne game da matsalar zuƙar taba sigari a cikin al'umma saɓanin  wasu keɓantattun wurare da doka ta tanada. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce a duk shekara sama da mutane miliyan 8 ne ke mutuwa sanadiyar shakar hayakin taba sigari kuma daga cikin wancan adadi, akwai sama da yara dubu 65 waɗanda lamarin ke shafa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

page 2 from 2