Al'adun Gargajiya

Yadda tsamin alaƙar gwamnati da Sarakuna ke raunata Masarautun gargajiya

Informações:

Synopsis

Shirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa a yau mayar da hankali kan rashin jituwar dake faruwa tsakanin gwamnoni a Najeriya da kuma ɓangaren Sarakunan gargajiya wanda har takai ga wasu jihohin na rushe Masarautu suna kuma kirkirar sababbi. A ‘yan shekarun nan, an sami irin wanann takun saka a jihohi irin Kano da Sokoto da Adamawa da kuma Katsina dukkaninsu a sassan Arewacin Najeriyar, inda masana tarihi da al’adu ke kallon al’amarin a matsayin barazana ga tsarin Sarautar mai dogon tarihi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.