Al'adun Gargajiya

Muhawwara akan bambamci da kamanceceniya tsakanin Shata da Rarara

Informações:

Synopsis

Shirin al’adu na wannan makon ya waiwayi al’adar waƙoƙin Hausa ne da kuma tasirin Mawaƙan da suke rera su waƙoƙin a fannonin rayuwa daban daban.  A baya bayan nan aka tafka muhawara tsakanin wasu masana guda biyu na Adabin Hausa wato Dakta Abdul-Shakur Yusuf Ishaq na Jami’ar Jihar Kaduna da kuma Dakta Mu’azu Sa’adu Kudan na Jami’ar Sule Lamiɗo da ke Kafin Hausa a jihar Jigawa, waɗanda suka baje iliminsu a kan matakin shahara, da kamance-ceniya da kuma banbanci a tsakanin Marigayi Mamman Ibrahim Yero da aka fi sani da Mamman Shata ko kuma Shata mai Ganga  da kuma Dauda Adamu Kahutu Rarara da a halin yanzu zamani ke tafiya da shi.