Al'adun Gargajiya

Yadda sana'ar kaɗi ke gab da gushewa tsakanin al'ummar Hausawa

Informações:

Synopsis

Shirin al'adunmu na gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya mayar da hankali ne kan gushewar sana'ar kaɗi a ƙasar Hausa duk da kasancewarta guda cikin sana'o'in Hausawan suka gada kaka da kakanni. Galibi sana'o'in Hausawa na tafiya ne da tsarin rayuwa da zamantakewar jama'a, cikin wannan kuwa har da sana'ar kaɗi wadda galibi dattawa Mata suka fi ƙwarewa akai, kodayake wannan sana'a na gab da gushewa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.