Synopsis
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.
Episodes
-
Yadda satar amsa tsakanin dalibai ke yiwa ilimi illa musamman a Najeriya
20/05/2025 Duration: 09minShirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali kan Illonlin satar amsa tsakanin Dalibai a yayin rubuta jarabawa. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna
-
Shirin gwamnatin Najeriya na dawo da tsarin koyarawa da harshen uwa
13/05/2025 Duration: 10minA wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan, shawarar gwamnatin tarayyar Najeriya ta dawo da tsarin amfani da harshen uwa a makarantun firamare da ke fadin kasar. Tsarin amfani da harshen uwa a makarantun firamare, wani tsari ne da aka gabatar a shekarar 2022, wadda ke da nufin inganta amfani da harsunan uwa a matsayin harshen koyarwa a makarantun firamare. Sai dai, a wancan lokaci da aka kaddamar da manufar za a yi amfani da ita ne akan Yara yan aji daya zuwa na makarantun firamare.Hakan kuwa ya biyo bayan bincike-bincike da aka gudanar wanda ya nuna cewa rashin fahimtar darusan da ake koyarwa da harshen Ingilishi ya bada gudunmowa wajen barin Yara makaranta da kuma haifar da koma-bayan ilimi a Najeriya.Sai da masana sun bayyana wasu ƙalubale da za a iya fuskanta da suka hadar da rashin wadatattun kayan koyarwa, da matsalolin zabar babban yare a cikin al'ummomi da ke amfani da harsuna da yawa.
-
Ɓangaren ilimin wasu jihohin Najeriya sun gaza samun tallafin gwamnatin ƙasar
06/05/2025 Duration: 10minShirin na wannan mako ya duba dalilan da suka sanya bangaren ilimi a matakin farko a Najeriya na matakin jihohi ya gaza samun gajiyar tallafin da zai taimaka wajen bunkasa karatun kananan yara, duk da makudan kudaden da gwamnatin ƙasar ta ware a matsayin tallafi. Bisa ga kididdigar da aka yi a baya-bayan nan, akwai yara fiye da miliyan 10 da ya kamata a ce suna makaranta a Nigeria amma a halin yanzu yawo su ke yi loko-loko ba tare da samun kowani irin nau’in ilimi ba.‘Yan kalilan din da suke samun halartar makaranta, mafi yawan su na fama da rashin wadatattun kayan karatu, kama daga azuzuwa, kayan koyarwa, kujeru da kuma uwa uba kwararrun malamai.
-
Ƙalubalen da suka dabaibaye harshen Hausa ta fuskar magana- Kashi na 2
29/04/2025 Duration: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya ɗora ne akan shirin makon jiya sai dai a wannan karon shirin ya karakata ne ga ɓangaren yadda matasa ke sauya wasu kalmomin Hausa ta hanyar yi musu ƙawance da wasu yaruka su bayar da wata kalma da za ta bayar da ma'anar da za a fahimci abin da ake nufi cikin sauƙi. Idan mai sauraro na biye da shirin na Ilimi Hasken Rayuwa a makwannin baya-bayan nan yana ci gaba da bibiyar dokoki ko kuma ladubban rubutu da karatu baya ga magana da harshen na Hausa, harshen da ake ci gaba da ganin bunƙasarsa ba kaɗai a nahiyar Afrika ba, harma da sauran nahiyoyi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Kalubalen da suka dabaibaye harshen Hausa ta fuskar rubutu - kashi na 2
22/04/2025 Duration: 10minShirin na yau, ya ɗora ne akan kashi na farko da muka gabatar a makon jiya, wanda ya yi duba game da yadda harshen Hausa ya bunkasa a lokutan baya, da muhimmacinsa, baya ga matsalolin da yake fuskanta da ma kalubalen da Rubutun Hausa ke fuskanta a kafofin sada zumunta. Masana sun bayyana ka'idojin rubutun Hausa, a matsayin wani yanayi na lura tare da kiyaye ka'idojin harshen Hausa a rubuce domin samun damar isar da sakon da marubuci ke nufi zuwa ga mai karatu daidai ba tare da dungushe ko sauya ma'anar da marubuci ke nufi ba. A cewar masanan kiyaye ƙa'idodin rubutun yana kuma samar da saukin fahimtar karatu daga mai karantawa.Ko da a kafafen yada labarai, rashin kiyaye ka'idojin rubutun Hausa yakan taka rawa wajen sauya ma'anar labari, to ko ya masu bibiyar shafukan yanar gizo na kafafen watsa labarai ke ji idan suka ga ba a yi amfani da harufa masu lanƙwasa ba kamar Ɓ da Ɗ da kuma Ƙ? Ga abinda wasu ke cewa.
-
Ƙalubalen da suka dabibaye harshen Hausa ta fuskar rubutu - Kashi na 1
15/04/2025 Duration: 09minShirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon shirin ya sauya salo zuwa mai dogon zango ta yadda zai tattauna da masu ruwa da tsaki a kan bunƙasar harshen Hausa da matsalolin da ya ke fuskanta da dalilan da suka haifar da matsalolin, da dai sauran muhimman batutuwa da suka shafi harshen na Hausa. Harshen Hausa, harshe ne da yake da tsohon tarihi wanda ya shafe ɗaruruwan shekaru ana magana da shi, wanda alƙaluma suka tabbatar da cewar zuwa yanzu miliyoyin mutane ne ke magana da harshen a sassan duniya.Wani rahoto da aka wallafa a shekarun baya bayan nan ya nuna cewar a halin yanzu Harshen Hausa ne Harshe na 11 da aka fi amfani da shi a duniya, zalika an yi ƙiyasin cewar mutane miliyan 150 ne ke magana da shi a sassan Duniya.Masana na kallon waɗaccan alƙaluma a matsayin dallilan da suka sanya harshen na Hausa yin shaharar ta kai ya yi gogayya da dukkanin manyan harsunan duniya, lura da yadda harshen ke da yalwar kalmomi da za a iya sarrafa su gami da bayyana kowanne irin tunani da su, walau
-
Yadda ɗalibai a Bauchi ke watsi da karatu don shiga aikin tonon ma'adinai
01/04/2025 Duration: 10minShirin wannan makon zai yi dubi ne akan yadda ɗalibai a jihar Bauchi ke yin watsi da karatu don shiga aikin tonon ma'adinai.Jihar Bauchi, ta yi ƙaurin suna a baya a matsayin wadda ke sahun gaba wajen yawan yaran da suka yi watsi da makarantunsu tare da rungumar harkar tonon ma’adinai don samun dogaro da kai.Dalili ke nan da fiye da rabin daliban wasu makarantun firamare a jihar, suka bar zuwa makaranta inda suka karkatar da hankali kan harka haƙon ma’adanan.
-
Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin ɗaukar nauyin karatun ƴaƴa mata zuwa PHD
25/03/2025 Duration: 09minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya maida hankali ne kan shirin da gwamnatin jihar Jigawa ta ƙaddamar, na ɗaukar nauyin karatun ‘ya’ya mata daga Firamaren har zuwa karatun Digirin Digirgir, shirin da ta ce tana fatan zai zaburar da ƙarin mata da iyayensu wajen duƙufa neman ilimi, ba tare da fargabar fuskantar ƙalubale na rashin ƙarfi ta fuskar tattalin arziƙi ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare Nura Ado Suleiman.........
-
Gwamnatin Ghana na nazarin yiwuwar fara bayar da ilimin Sakandire kyauta
04/03/2025 Duration: 09minShirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan shirin gwamnatin Ghana na fara bayar da ilimin Sakandire kyauta, kodayake an faro da sauraren ra'ayin jama'a kan wannan shiri wanda ma'aikatar ilimin ƙasar ta bijiro da shi. Bayanai sun ce baya ga bayar da ilimin kyauta, tsarin zai kuma kawo gyara a yanayin bayar da ilimi musamman a manyan makarantun ƙasar ta Ghana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
-
Yadda matasa a Najeriya suka ƙirƙiri injin da ke tsince tsakuwa daga Shinkafa
25/02/2025 Duration: 09minA wannan makon, shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Aisha Shehu Kabara ya mayar da hankali kan yadda wasu matasa suka ƙirƙiri wani nau'in inji da ke cire tsakuwa daga jikin shinkafa, wanda zai taimaka matuƙa wajen samar da tsaftatacciyar shinkafa. Kafin wannan hoɓɓosa daga matasan, akan shigo da irin injinan ne daga ƙasashe irin China don sauƙaƙawa Manoma.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Gwamnatin Najeriya ta ɗaga likafar Kwalejin Kimiyyan Lafiya ta Tsafe zuwa Jami'a
18/02/2025 Duration: 09minShirin “Ilimi Hasken Rayuwa” namu na wannan mako, ya yada zango ne a tarayyar Najeriya, inda shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan ƙudurin samar da sabuwar jami’a kimiyyan lafiya da fasaha ta tarayya wato Federal University of Health Science and Technology a garin Tsafe na Jihar Zamfara, bayan tsallake dukkan matakan majalisa dokokin ƙasar. Wannan saka nannu na shugaban ƙasar ya yi zai bada damar ƙara inganta harkan kiwon lafiya ta hanyar samar da kwararru.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.........
-
Matsin rayuwa na barazanar gurgunta karatun ƙananan yara a Najeriya
11/02/2025 Duration: 09minShirin ''Ilimi Hasken Rayuwa'' tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan yadda halin matsin rayuwa ke yin tasiri a kan karatun yara ƙanana lamarin da ya sa kaso mai yawa daga cikinsu ba sa samun cikakkiyar fahimta a kan darussan da ake koya musu, saboda dalilai da dama masu alaka da matsin rayuwar. Baya ga batun ci a koshi dai, yanyayin da yara ƙanana ke tafiya makarantunsu a yanayin da ake ciki ma lamari ne da ya kamata a mayar da hankali akai, la’akari da cewar a wasu lokutan ɗan hakin da ka raina kan tsone maka ido.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
-
Yadda za'a koya wa yara iya karatu tun daga matakin farko a Najeriya
04/02/2025 Duration: 10minShirin ilimi hasken rayuwa na wannan lokaci ya mayar da hankali kan yadda za'a bi ƙa'idoji da hanyoyi domin koya wa yara iya karatu a matakin farko a Najeriya. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
-
Gasar HIFEST karo na bakwai a Najeriya
28/01/2025 Duration: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, ya yi duba ne, kan yadda wata kungiya a Najeriya, ke karfafa gwiwar daliban sakandire kan yadda za su bayyana baiwar da suke da ita, musamman a bangaren ilimin fasaha.
-
Mahimmancin kwalejojin fasaha a Najeriya wajen bunƙasar ɓangaren ilimin kimiyya
24/12/2024 Duration: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya yi nazari ne kan mahimmancin kwalejojin fasaha na Najeriya ga bunƙasar ɓangaren ilimin kimiyya da fasaha a ƙasar, da kuma kalubalen da suke fuskanta a halin yanzu, sai kuma duba hanyoyin da za a bi don farfaɗo da martabarsu. Ku latsa almar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman............
-
Tasirin da salon koyarwa ke da shi wajen baiwa ɗalibai ingantatcen ilimi
10/12/2024 Duration: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan mako, ya tattauna ne a kan salon koyarwa tun daga matakin makarantu na ƙasa wato ‘Method of Teaching’ a turance, da tasirin da wannan salo ke da shi kan bayar da ilimi. Salo ko kuma dabarun koyarwa matakai ne ko tsarin da malamai ke amfani da su wajen koyar da ɗalibai darussa, a kuma tabbatar da cewa ɗaliban sun fahimci darasin da ake yi musu. A mafi yawan lokuta waɗannan dabaru sukan bambamta a tsakanin darussa, zalika ya danganta da matakan ilimi daga ƙasa, da na tsakiya zuwa na sama.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.......
-
Rashin malamai ya tilasta iyaye janye yaransu daga makarantu a kudancin Najeriya
06/11/2024 Duration: 09minShirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda iyaye a yankin kudancin ƙasar ke janye yaransu daga Makarantu saboda ƙarancin makarantu a yankin. Jihar Abia na sahun ƴan gaba gaba da ke fama da wannan matsala inda a baya-bayan nan aka tarin yaran da suka daina zuwa makaranta.
-
Gwamnatin Bauchi na shirin mayar da yara fiye da miliyan 1 makarantu
29/10/2024 Duration: 09minShirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda gwamnatin jihar Bauchi a Najeriya ke yunƙurin mayar da yara fiye da miliyan guda makaranta a wani yanayi da ake ganin ƙaruwar yaran da basa zuwa makaranta a yankin arewacin kasar. Tuni masu ruwa da tsaki a wannan yanki suka yi maraba da matakin gwamnatin ta Bauchi, lura da yadda yunƙurin zai taimaka matuƙa wajen rage ɗimbin yaran da ke gararamba ba tare da zuwa makaranta ba a Arewacin na Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
-
Ɓanagrorin ilimi sun koka da matakin JAMB na durkusar da harshen Faransanci
24/10/2024 Duration: 10minSannu a hankali darussan nazarin harshen faransanci na kara karbuwa a manyan makarantun Nigeria, sai dai kuma, wani matakin da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB a Nigeria, ta aiwatar, na cire takardar shaidar share fagen shiga jami’a ta karatun harshen faransanci, daga cikin darussan da hukumar ta JAMB ke bayar da guraben karatunsu a manyan makarantu ya daga hankalin masu ruwa da tsaki.
-
Yadda wasu gwamnoni a Najeriya ke biris da yaran talakawa da suka tura karatu wasu kasashe
15/10/2024 Duration: 10minShirin na wannan rana ya duba yadda wasu gwamnonin a Najeriya ke daukar alhakin tura yaran talakawa wasu kasashe domin karatu amma kuma daga bisani sai gwamnatin ta yi biris da sha'aninsu.