Synopsis
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.
Episodes
-
Yadda tsadar lantarki ke kassara harkokin karatun manyan makarantun Najeriya
16/07/2024 Duration: 10minA wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne kan yadda tsadar kuɗin wutar lantarki ke gurgunta harkokin karatu a manyan makarantun Najeriya.Kamar yadda aka sani, harkokin gudanarwar yau da kullum na manyan makarantu ba za su taɓa yiwu wa yadda ya kamata ba, muddin babu ingantacciyar wutar lantarki. To sai dai, baya ga rashin tsayayyiyar wutar a kusan manyan makarantun Najeriya, wata matsalar kuma ita ce ta tsadar wutar a sakamakon ƙarin farashin kuɗin wutar lantarki da gwamnatin ƙasar ta yi.Wannan dalili ne ya sanya ƙungiyar shugabannin jami’o’in Najeriya, ta yi kashedin cewa jami’o’in tarayyar ƙasar aƙalla 52 ka iya durƙushewa nan ba da jimawa ba, a sakamakon tsadar kuɗin wutar.Shugabannin Jami’o’in na Najeriya, sun yi wannan gargaɗi ne bayan wani sabon ƙari na kashi 300 da aka yi musu a kwanakin baya.Kuna iya latsa alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin...
-
Dalilan mummunar faduwar jarabawa da daliban jamhuriyar Nijar suka yi a bana
09/07/2024 Duration: 09minShirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda dalibai a jamhuriyar Nijar suka yi mummunar faduwa a sakamakon jarabawar karshe ta makarantar Sakandare. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadir Haladu kiyawa
-
Yadda ayyukan ƴan ta'adda suka kassara harkokin Ilimi a Arewacin Najeriya
02/07/2024 Duration: 09minA wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan yadda hare-haren ‘yan ta’adda suka kassara harkokin ilimi a arewacin Najeriya, shekara 10 kenan da 'yan ta'adda suka fara kai hari kan makarantu a Najeriya, lamarin da ya fara faruwa a shekarar 2014 a makarantar sakandaren ‘yan mata ta garin Chibok da ke jihar Borno a Arewa maso gabashin kasar. Bincike ya nuna cewa, tun bayan harin na 2014, 'yan ta'adda sun ci gaba da kai makamancinsa a kimanin makarantu 17, waɗanda suka haɗa da makarantun Firamare da sakandare da ma manyan makarantun gaba da sakandare, inda suka yi garkuwa da dalibai da dama, an sako wasu bayan biyan kuɗin fansa, wasu kuwa suna rike a hannunsu har zuwa yanzu. Cikin shekaru goma da fara ƙaddamar da irin wannan ta'addanci kan makarantu da ɗalibai, masana sun bayyana shakku kan gwamnatin Najeriya tare da zarginta da nuna halin ko in kula kan ilimi tare da rayukan al'ummar kasar musamman ɗalibai. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...