Synopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodes
-
Ra'ayoyin masu sauraren kan yadda ɗimbin mutane suka rasa ayyukansu a Nijar
25/08/2025 Duration: 11minA jamhuriyar Nijar, dubban mutane ne suka rasa ayyukansu yayin da ɗimbin ƴan gudun hijira suka daina samun tallafi, bayan da mahukunta suka kori mafi yawan ƙungiyoyin agaji daga gudanar da ayyukansu a cikin ƙasar. Bayan korar waɗannan ƙungiyoyi da ke taimaka wa ƴan gudun hijira, a mafi yawan yankuna har yanzu gwamnatin ta gaza samar da tsarin da zai maye gurbin waɗannan ƙungiyoyi don agaza wa jama’a. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin....
-
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa da dama
22/08/2025 Duration: 06minYau Juma'a rana ce da mukan baiwa masu saurarenmu damar tofa albarkacin bakinsu a cikin shirinmu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya. Danna alamar saurare domin jin cikaken shirin tare da Nasiru Sani
-
Ra'ayoyin masu saurare kan alfanun sulhu da 'yanbindiga ko akasanin haka a Najeriya
21/08/2025 Duration: 10minA Najeriya muhawara ta ɓarke game da buƙatar sulhu da ƴan ta’adda maimakon amfani da ƙarfin Soji, kodayake an samu mabanbantan ra’ayoyi daga ɓangaren masana a fannin na tsaro lura da yadda suka ce irin wannan sulhu ya gaza amfanarwa a yankuna da dama duk da cewa anga alfanunsa a wasu yankunan. Yaya kuke kallon wannan batu? Shin kuna ganin sulhu ko kuwa amfani da ƙarfin soji shi ne mafi a’ala wajen yaƙi matsalolin tsaron Najeriyar? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkaci bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza....
-
Ra'ayoyin masu saurare kan shirin rungumar GMO a Najeriya
19/08/2025 Duration: 10minLura da yadda jama’a ke ɗari-ɗari a game da kayan abincin da aka sauya wa ƙwayoyin halitta da ake kira GMO, wannan ya sa mahukunta a Najeriya ke neman yin amfani da malaman addini domin gamsar da jama’a su rungumi irin wannan abinci. Abin neman sani a nan shi ne, shin ko kun fahinci abin da ake kira GMO? Ko a shirye ku ke domin karɓar nau’in abincin da aka canza wa ƙwayoyin halitta? Anya yin amfani da malaman addini zai sa jama’a su amince da shi a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...