Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 3:59:39
  • More information

Informações:

Synopsis

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu

Episodes

  • Kan yadda EFCC ta kwato Naira tiriliyan guda daga hannun ɓarayin gwamnati

    11/03/2025 Duration: 09min

    Hukumar Yaƙi da Rashawa a Najeriya EFCC, ta ce a cikin shekarar ta 2024 da ta gabata, ta yi nasarar ƙwato kusan Naira tiriliyan ɗaya daga hannun barayi da masu handame dukiyar al’umma. EFCC ta ce ko a gaban kotu ma, ta samu nasarori sama da sau dubu huɗu akan masu cin rashawa da kuma ƴan damfara cikin shekarar da ta gabata.Abin tambayar shine, ko aikin hukumar na gamsar da 'yan Najeriya?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakakken shirin.

  • Kan yadda direbobin manyan motoci ke fuskantar kisa daga 'yan awaren Biafara

    04/03/2025 Duration: 10min

    Ƙungiyar direbobin motoci a Najeriya, ta buƙaci mahukunta su ɗauki matakan kawo ƙarshen kisan da ƴan awaren Biafra ke yi wa direbobin manyan motoci a duk lokacin da suke ratsa yankin kudu maso gabashin ƙasar. Ƙungiyar ta ce an kashe mambobinta sama da 50, kuma 20 daga cikinsu an kashe su ne a shekarar 2024, sannan aka kwashe kayayyaki da kuma ƙona motocinsu.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya

    28/02/2025 Duration: 10min

    A yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan yawaitar masu ta'ammali da ƙwayoyi a Arewacin Najeriya

    27/02/2025 Duration: 10min

    Aƙalla 40% na mazauna yankin arewa maso yammacin Najeriya ne ka tu’ammuli da miyagun ƙwayoyi, kuma kusan 28 cikin ɗari suna zaune ne a jihar Kaduna kamar dai yadda rahoton hukumomin da yaƙi da wannan matsala ya nuna.  Hakazalika, mutum 1 cikin 7 a yankin arewa maso yammacin ƙasar suna tu’ammali da miyagun ƙwayoyin a cewar rahoton.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbata

    21/02/2025 Duration: 09min

    A yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan tarar da za a ci masu satar lantarki a Najeriya

    20/02/2025 Duration: 09min

    Hukumar Ƙayyade Farashin Wutatar Lantarki a Najeriya, sanar da sabon tsarin biyan tara a kan waɗanda ke satar makamashin lantarki a ƙasar. Tarar ta kama daga Naira dubu 100 zuwa dubu 300 daidai da irin salon da mutum ya yi wajen sada gidansa da wannan makamashi.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan saukar farashin kayan abinci a Najeriya

    19/02/2025 Duration: 09min

    Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa a Najeriya, ta ce farashin kayan abinci ya sauka a cikin watan Janairun da ya gabata da 10% idan aka kwatanta da na wata Disamba. To waɗannan dai bayanai da hukuma ta fitar, saboda haka za mu so jin ra’ayoyinku a game da wannan rahoto.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Abida Shu'abu Baraza...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan kashe maƙudan kuɗaɗe don inganta lantarki a Najeriya

    18/02/2025 Duration: 10min

    Alƙalumma na nuni da cewa a cikin shekaru 10 da suka gabata, an kashe aƙalla Naira Tiriliyan 7 da bilyan 200 a matsayin tallafi da nufin inganta sanar da wutar lantarki a Najeriya. To sai dai a zahirin ana cewa har yanzu wannan ɓangare na ci gaba fama da matsaloli masu tarin yawa, yayin da a ɗaya ɓangare farashin wutar ya ninka ninkin ba ninkin.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta

    07/02/2025 Duration: 11min

    A yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...

  • Shirin ra'ayoyin ku masu sauraro a yau.

    03/02/2025 Duration: 09min

    a yau shirin namu na ra'ayoyin ku masu sauraro ya yi dubu ne akan Shin ko menene ra'ayin ku a game da batun tattaunawa da 'yan bindiga.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta

    31/01/2025 Duration: 09min

    A yau juma'a kamar yadda aka saba kuna aiko mana da saƙonnin ra'ayoyinku kan abubuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, kama daga fannin tattalin arziki, tsaro, lafiya, siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan shirin samar da lantarki ga gidaje 300M a Afirka

    30/01/2025 Duration: 09min

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake jaddada aniyarsa ta inganta samar da wutar lantarki a faɗin ƙasar. Tinubu ya bayyana haka ne wajen taron ƙasashen Afirka wanda ya mayar da hankali akan yadda za a samar wa aƙalla mutane miliyan 300 wutar lantarki a nahiyar baki ɗaya. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan cikar wa'adin ficewar ƙasashen AES daga ECOWAS

    29/01/2025 Duration: 09min

    Yau 29 ga watan Janairu wa’adin farko da kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso suka bayar na ficewa daga kungiyar ECOWAS ya cika, abinda ke tabbatar da raba garin bangarorin biyu dangane da cikar wannan wa’adi, Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta

    24/01/2025 Duration: 10min

    A yau juma'a kamar yadda aka saba kuna aiko mana da saƙonnin ra'ayoyinku kan abubuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, kama daga fannin tattalin arziki, tsaro, lafiya, siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...

  • Yadda aka fara samun saukin farashin kayayyakin abinci a Najeriya

    23/01/2025 Duration: 10min

    Rahotanni daga wasu sassan Najeriya ciki har da babbar kasuwar kayan abinci dangin hatsi ta Dawanau da ke Kano na cewa an fara samun sauƙin farashin kayayyakin abincin, idan aka kwatanta da yadda al’amarin yake a watannin baya. Lamarin dai ya haifar da muhawara akan dalillan da suka janyo saukin farashin kayana abincin da ɗorewar hakan.Abin tambayar shine, ko al'umma sun gamsu da wannan rahoto, ko kuma har yanzu anan nan a gidan jiya?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan ficewar Amurka daga WHO

    22/01/2025 Duration: 09min

    A ƙasar Amurka, bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaba ƙasa na 47, Donald Trump, ya rattaba hannu kan wasu gomman dokokin zartawa na ikon shugaban ƙasa, ciki har da janye ƙasarsa daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), kamar yadda ya yi a wa’adin mulkinsa na farko, kafin magabacinsa Joe Biden ya maido da ƙasar ciki. Wasu na ganin wannan mataki zai yi illa ƙwarai ga ɗorewar hukumar wajen gudanar da ayyukan ta a duniya, duba da kaso mai tsoka da Amurka ke bayarwa wajen gudanar da ayyukan WHO ɗin.Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan sabuwar dokar Nijar na hukunta baƙi marasa takardu

    15/01/2025 Duration: 09min

    A wannan makon ne gwamnatin sojin Nijar ta gabatar da wata sabuwar doka da ke tilastawa baƙi da ke neman zuwa ƙasar da su tabbatar sun samu takardun izini da suka dace, tare da gargadi ga su ma ƴan ƙasar da su yi hattara wajen ƙarbar baƙunci baƙi da ke shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba. Sabuwar dokar ta soji ta tanadi hukunci mai tsauri ga waɗanda suka saɓa umarnin a bangarorin baƙi da su kansu ƴan ƙasar, wanda ya ƙunshi hukuncin ɗauri a gidan yari da kuma tara.Gwamnati da wasu ƴan ƙasar na cewa anyi hakan ne saboda dalilai na tsaro, yayin da wasu ke danganta hakan da tsoro da fargaba, to ku ya kuka kalli wannan mataki?Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.....

  • Ra'ayoyin masu saurare kan hare-haren soji da ke kashe fararen hula bisa kuskure

    14/01/2025 Duration: 10min

    A baya-bayan hare-haren sojojin Najeriya kan ƴan ta’adda na shafar fararen hula musamman ƴan sa kai da ke taimakawa wajen yaƙar matsalolin tsaro. Matsalar na ƙara yawaita inda a kwanan nan sojojin suka kai hari a jihohin Sokoto da Zamfara wanda ya halaka fararen hula fiye da 100, yayin da a kowane lokaci sojojin kan musanta hakan , daga baya kuma su ce za su gudanar da bincike.Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan sallamar tuɓaɓɓun ƴan Boko Haram da aka yi a Nijar

    13/01/2025 Duration: 09min

    A wani yanayi da ba safai aka saba gani ba, mahukuntan Nijar sun sallami tuɓaɓɓun mayaƙan Boko Haram aƙalla 124 ciki har da ƙananan yara 44, waɗanda aka basu horan sauya ɗabi’u don komawa rayuwar fararen hula. Wannan shi ne karon farko da ake ganin irin hakan, tun bayan makamancin yunƙurin da hamɓararren shugaban ƙasar Bazoum Muhammad ya yi watanni ƙalilan gabanin hamɓarar da shi.Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi a cikin shirin...

  • Yadda ake rige-rigen neman aiki a hukumar kwastam da ke Najeriya

    09/01/2025 Duration: 10min

    Kamar yadda labari ya karaɗe kafafen yada labarai, ƙaasa da mako guda bayan da hukumar kwastan a Najeriya ta sanar da buɗe shafin yanar gizo don aikewa da takardun neman ɗaukar jami’ai kimanin dubu 4, sama da masu neman wannan aiki dubu dari 5 ne suka gabatar da buƙatunsu. Wannan al’amari ne da ke faruwa a kowace ma’aikata a duk lokacin da aka sanar da buƙatar ɗaukar ma’aikata.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza.

page 1 from 2