Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Ra'ayoyin masu saurare kan kama Simon Ekpa mai fafutukar kafa ƙasar Biafra

Informações:

Synopsis

Kotun ƙasar Finland ta ɗaure Simon Ekpa mai fafutukar kafa ballewar Biafra daga Najeriya shekaru 6 a gidan yari, saboda samun sa da laifufukan ta’addanci.   Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin ake ci gaba da tsare ɗaruruwan mutane a gidajen yarin Najeriya bisa zargin aikata ta’addanci, amma kotuna sun gaza hukuntar da su. Shin ko me za ku ce a game da wannan hukunci da kotun ƙasar Finland ta yanke? Meye ra’ayoyinku a game da gazawar kotunan Najeriya wajen hukunta waɗanda ake tuhuma da aikata irin waɗannan laifuka a cikin gida? Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu