Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Ra'ayoyin masu saurare kan afuwar da shugaban Najeriya ya yiwa wasu mutane 175

Informações:

Synopsis

Ra’ayoyi na ci gaba da bayyana dangane da afuwar da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi wa mutane 175 da aka kama da laifuka daban daban. Daga cikin waɗanda aka yi wa afuwar har da waɗanda aka yankewa hukuncin kisa, da safarar makamai da miyagun ƙwayoyi da dai sauransu. Shin ko me za ku ce a game cancanta ko kuma rashin dacewar yin wannan afuwar? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...