Wasanni
Sharhi kan yadda aka kammala wasannin zuwa gasar AFCON da za a yi a Morocco
- Author: Vários
- Narrator: Vários
- Publisher: Podcast
- Duration: 0:10:00
- More information
Informações:
Synopsis
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan yadda aka kammala wasannin neman gurbin shiga gasar lashe kofin Afrika. Kuma a tsakiyar makon daya gabata ne aka kammala wasannin neman gurbin zuwa gasar cin kofin AFCON da ke gudana tsakanin ƙasashen Afrika, gasar da Morocco za ta karɓi baƙunci a watan Disamban shekarar 2025. A yanzu dai dukkanin ƙasashe sun san makomarsu kuma ƙasashen 24 da za a ga haskawarsu a gasar ta baɗi sun ƙunshi ita mai masaukin baƙi Morocco da Burkina Faso da Kamaru da Algeria da Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo da Senegal da Masar da Equatorial Guinea da Cote d’Ivoire da Uganda da Afrika ta Kudu da Gabon da Tunisia da Najeriya.Sauran sun ƙunshi Zambia da Mali da Zimbabwe da Tsibirin Comoros da Sudan da Benin da Tanzania da Botswana da kuma Mozambique, a wani yanayi da Bostwana ke samun tikitin gasar karon farko bayan dakon shekaru 12.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh........