Synopsis
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Episodes
-
Makomar ƙasashen Najeriya, Senegal da Afrika ta Kudu a gasar cin kofin Duniya
13/10/2025 Duration: 09minShirin a wannan mako ya mayar da hankali ne kan wasannin neman tikitin zuwa gasar cin kofin Duniya ta 2026 da ƙasashen Amurka, Mexico da Canada za su karɓi baƙunci. A Nahiyar Afrika tuni dai wasu ƙasashe suka sami tikitin zuwa gasar da suka haɗar da Morocco da Tunisia da Aljeriya da Ivory Cost, sai dai ƙasashen Najeriya da Afrika ta Kudu da kuma Senegal na cikin halin rashin tabbas, sai dai a wannan Talata ne za su san makomarsu. Latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Abubakar Isah Ɗandago..................
-
Gudummawar da cibiyoyin horar da matasa ke baiwa ƙwallon Ƙafa a Najeriya
06/10/2025 Duration: 09minShirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan lokaci za yi duba ne kan irin gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon Ƙafa ke bayarwa wajen zakulo matasan ƴan wasa da horar da su a Najeriya. A wani bangare na gudummawarsu ga ci gaban wasan kwallon kafa a Nigeria, ɗai-ɗaikun jama’a da ƴan kasuwa kai harma da tsofin ƴan wasan tawagar Super Eagles ta ƙasar, sun fara kafa cibiyoyi masu zaman kan su, da su ke zakulowa tare da horar da matasa don yin fice a harkar ta kwallon ƙafa. Irin wadannan cibiyoyin horar da matasa wasan na kwallon kafa da a turance ake kira FOOTBALL ACADEMY, kan shiga birane da karkara don tuntubar ƙanana da matsakaitan club-club, domin samun ƴan wasan daga wajen su da za a yi rijistarsu a wannan cibiya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..
-
Mahangar masana game da yadda Dembele ya lashe kyautar Ballon d'Or a bana
29/09/2025 Duration: 10minShirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali kan yadda ɗan wasan gaba na PSG ɗan Faransa Ousmane Dembele ya lashe kyautar Ballon d'Or a bana, bayan nasarar shi ta lashe kofuna da dama cikin kakar da ta gabata da ƙungiyar tasa da ke birnin Paris. Duk da cewa anjima ana hasashen Dembele ya lashe wannan kyauta lura da namijin ƙoƙarinsa a kakar da ta gabata, amma wasu na da ra'ayin cewa sam ɗan wasan bai cancanci wannan kyauta ba. Game da wannan saɓanin ra'ayi, shirin na Duniyar Wasanni ya tattauna da masana a fagen na wasanni waɗanda suka bayyana ra'ayoyinsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Adawar magoya bayan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙarawa gasar armashi
22/09/2025 Duration: 10minShirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya yi duba ne kan yadda adawar magoya bayan ƙungiyoyi ke karawa kwallon ƙafa tagomashi. Wasanni da dama ne dai ke samu karbuwa a duniya da suka haɗa da kwallon ƙafa da kwallon kwando da kwallon Cricket da Tennis da dai sauransu, amma kuma kowane wasa na da irin nashi magoya baya da suke matuƙar ƙaunarsa da so a duniya. Bincike ya nuna cewa babu wani wasa da ta fi kwallon kafa magoya baya a duniya, inda aƙalla mutane biliyan 3 da rabi ne ke sha'awar wasan baya ga ƴan kwallon kansu da suka kai miliyan 250, waɗanda hukumomin kwallon ƙafa a duniya FIFA ta yiwa rijista. Hatta a Najeriya nuna sha'awa na magoya baya ba ya misaltuwa, domin babu lungu da sako da wasan bai samu karɓuwa ba musamman ma wasannin nahiyar Turai da ya fi can hankali. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Makomar tawagar Najeriya a ƙoƙarin neman gurbin zuwa gasar lashe kofin duniya
15/09/2025 Duration: 09minShirin a wanan mako tare Khamis Saleh, ya yi duba ne kan makomar tawagar Najeriya a ƙoƙarin neman gurbin zuwa gasar lashe kofin duniya, inda a tsakiyar makon da ya gabata aka kammala wasannin na 8 na sharen fagen zuwa gasar lashe kofin duniya da ƙasashen Canada da Mexico da kuma Amurka za su karɓi bakunci a shekara mai zuwa. Kawo yanzu dai wasanni sun ɗauki zafi ganin cewa wasu daga cikin tawagogin ƙasashen sun fara jin kanshin halartar gasar, amma kuma wasu har yanzu tana ƙasa tana dabo. Latsa alamar sauri domin sauraron cikakken shirin.....
-
Yadda wasannin sharen fagen zuwa gasar cin kofin duniya ke gudana a Afrika
08/09/2025 Duration: 10minKawo yanzu dai wasanni sun ɗauki zafi ganin cewa wasu daga cikin tawagogin ƙasashen sun fara jin kanshin halartar gasar, amma kuma wasu har yanzu tana ƙasa tana dabo. Tawagar ƙasar Morocco tuni ta samu nata tikitin bayan da ta haɗa maki 18, tazarar maki 8 tsakaninta da Tanzania. Tawagogin ƙasashe irinsu Masar da Algeria da Tunisia da Ghana da Afrika ta Kudu, duk da cewa akwai tazarar maki masu ɗan dama tsakaninsu da waɗanda ke mataki na biyu a rukunansu, har yanzu akwai sauran rina a kaba.
-
Yadda ake samun takun saƙa tsakanin ƙungiyoyi da 'yan wasa wajen canza sheƙa
01/09/2025 Duration: 10minShirin a wannan makon zayyi duba ne kan yadda ake samun takun saƙa tsakanin ƴan wasa da ƙungiyoyinsu a duk lokacin da suke son sauya sheƙa. A duk lokacin da a ka buɗe kasuwar sayen ƴan wasa a duniya, a kan samu takaddama lokaci zuwa lokaci tsakanin ƴan wasa da kuma ƙungiyoyin su saboda wasu ƙungiyoyi na kin amincewa da ƴan wasansu su sauya sheka lokacin da su kuma ƴan wasan ke son bari.
-
Sabon jagorancin ƙungiyar Ranchers Bees na ƙoƙarin farfaɗo da martabarta
25/08/2025 Duration: 09minShirin Duniyar Wasanni a wannan mako ya yi dubu ne kan amsar ragamar jagorancin ƙungiyar Ranchers Bees da ke jihar Kaduna a Najeriya, da ɗan wasan Super Eagles Sadiq Umar Jololo da kuma ɗan majalisar wakilai Hon. Bello El-Rufai suka yi. Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Ranchers Bees na cikin ƙungiyoyin kwallon ƙafa da suka yi suna a baya amma a ka daina jin ɗuriyarta a yan shekarun nan, duk kuwa da cewa har a Nahiyar Afrika baki ɗaya ƙungiyar ta yi fice. A baya dai ƙungiyar ta Ranchers Bees ta lashe kofin yankin Afrika ta yamma wato WAFU sannan a Najeriya kuwa ta lashe kofin kalubale FA cup da dama. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..............
-
Yadda wasanni suka gudana bayan fara sabuwar kakar ƙwallon ƙafa a Turai
18/08/2025 Duration: 10minShirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon ya mayar da hankali ne a kan yadda aka fara sabuwar kakar ƙwallon ƙafa a bana a manyan Lig-Lig na sassan nahiyar Turai. Manyan wasannin dai sun haɗa da na Firimiyar Ingila, La Ligar Spain, da kuma gasar Ligue 1 na ƙasar Faransa. Kamar yadda za a ji cikin shirin tare da Khamis Saleh, Liverpool ce ta fara buɗe sabuwar kakar wasa a Firimiyar Ingila inda ta lallasa Bournemouth da ƙwallaye 4-2.
-
Yadda wasanni ke ɗaukar hankalin matasa a lokacin hutu a Nijar
11/08/2025 Duration: 09minShirin a wannan makon zayyi duba ne kan yanda wasanni ke ɗaukan hankalin matasa a irin wannan lokaci na hutun ƴan makaranta a Nijar. A duk lokacin da aka yi dogon hutun ƴan makaranta a Jamhuriyar Nijar, wanda ke farawa daga watan Yuli zuwa Satumba. Irin wannan lokaci na zama wata babbar dama ga masu kula da ɓangaren wasanni iri daban daban, don suna samun ɗinbin matasa da ke nuna sha’awarsu a ɓangaren wasanni.
-
Yadda shugaban Najeriya ya tarbi tawagar Super Falcons bayan lashe gasar WAFCON
04/08/2025 Duration: 09minShirin a wannan makon zayyi duba ne kan karramawar da gwamnatin Najeriya ta yi wa tawagar Super Falcons na lashe gasar WAFCON. A makon da ta gabata ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya karrama ƴan wasan tawagar ƙungiyar kwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Falcons, bayan nasarar lashe kofin WAFCON karo na 10 daga cikin 13 da aka yi. Cikin kyautukan da gwamnati ta baiwa waɗannan ƴan wasa akwai lambar girmamawa na ƙasa wato OON da shugaban Tinubu ya baiwa dukkan ƴan wasan da masu horar dasu, hakazalika kowacce ƴar wasa ta samu dalan amurka dubu 100, da kuma karin naira miliyan goma-goma daga ƙungiyar gwamnonin Najeriya. Tuni dai shugaban hukumar wasani a Najeriya Shehu Dikko ya yaba da wannan nasarar da kuma irin karramawar da shugaban ƙasar ya yiwa ƴan wasan. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.
-
Yadda ta kaya a gasar lashe kofin Afirka ta mata
28/07/2025 Duration: 09minShirin Duniyar Wasanni a wannan makon tareda Khamis Saley yayi duba ne kan wasan ƙarshe na gasar lashe kofin mata ta Afrika WAFCON da aka yi a ƙarshen mako. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin......
-
Yadda RFI hausa Hausa ta ƙulla alaƙa da ƙano pillars
21/07/2025 Duration: 09mina cikin shirin Duniyar wasanni na yau zaku ji yadda sashin Hausa na RFI ya ƙulla yarjejeniyar Naira miliyan 100 da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars dake Arewacin Najeriya a ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2025. A latsa alamar sauti domin domin sauraren cikakken shirin.
-
Tasirin wasannin sada zumunta ga manyan ƴan wasa a lokacin hutun manyan Lig
07/07/2025 Duration: 10minShirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya mayar da hankali kan wasanni da ke gudana a lokacin hutu, ta yadda manyan ƴan wasa daga lig lig na Turai da sauran nahiyoyi ke komawa gida don doka wasannin sada zumunta a irin wannan lokaci, lamarin da ke nishaɗantarwa da kuma ƙara danƙon alaƙa tsakanin manyan ƴan wasan da masu tasowa. A cikin shirin zakuji tattaunawa da masana a fannin na wasanni da kuma tsaffin ƴan wasa game da muhimmancin irin waɗannan wasanni na sada zumunta. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Kwara da Rivers sun lashe kofin ƙalubale na Najeriya a bangaren Mata da Maza
30/06/2025 Duration: 09minShirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya mayar da hankali ne kan wasannin ƙarshe na gasar cin kofin ƙalubale na Najeriya, wadda yanzu ake kira President Federation Cup, da aka gudanar a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena da ke birnin Lagos. Da wasan mata aka fara, inda aka ɓarje gumi tsakanin ƙungiyar kwallon ƙafa ta Nasarawa Amazons da ke garin Lafia da Rivers Angels ta birnin Fatakwal a wansan ƙarshe karo na 10 a wannan gasa, ɓangaren mata. Ƴan matan Nasarawa ne suka fara saka ƙwallaye biyu a ragar Rivers, ƙwallayen da Rukayyat Shola Sobowole ta ci, a yayin da Taiwo Ajibade da Taiwo Afolabi suka farke wa Rivers. Haka dai aka tashi wannan wasa biyu da biyu, Rivers mairiƙe da kofin ta sake daukawa a wannan karon a bugun daga kai sai mai tsaron raga da ci 4 da 2. Bayan wasan na mata, da baye-bayen kyautuka ne aka shiga wasan maza, inda kungiyar ƙwallon ƙafa ta Kwara United ta garin Ilorin ta doke Abakaliki FC da ci 4 da 3 a bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da aka buga can
-
Shirye-shiryen sun yi nisa na fara gasar Firimiyar Najeriya ta baɗi
23/06/2025 Duration: 10minShirin Duniyar Wasanni a wanan mako ya yi dubu ne kan shirye-shiryen fara gasar Firimiyar Najeriya ta kaka mai zuwa, kuma tuni hukumar shirya gasar Firimiyar Najeriya wato NPFL, ta sanya 22 ga watan Agusta mai zuwa a matsayin ranar soma kaka ta baɗi. An dai ji shugaban hukumar shirya babbar gasar ta Najeriya Gbenga Elegbeleye na cewar, suna duba yuwuwar soma amfani da na’urar VAR a gasar mai zuwa, baya ga kuma inganta kayayyakin gudanarwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............
-
An bude gasar lashe ƙofin duniya ta kungiyoyi a Amurka
16/06/2025 Duration: 09minShirin Duniyar wasanni na wanan makon tare da Khamis Saleh ya maida hankali ne akan gasar lashe ƙofin duniya ta kungiyoyi da aka bude a karshen mako a ƙasar Amurka dama sauye -sauyen da aka samu a bana. Ku shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shiri........
-
Yadda ta kaya a gasar sukuwar dawaki da aka gudanar a birnin Zazzau
09/06/2025 Duration: 09minShirin Duniyar Wasanni a wannan makon yi duba ne kan gasar sukuwar dawaki da aka gudanar a birnin Zazzau da ke tarayyar Najeriya, inda ƙasashe 5 da suka haɗa da Nijar da Kamaru da Chadi da Burkina Faso da Mali da kuma mai masaukin baƙi Najeriya suka fafata. Wannan ne dai karo na farko da aka gudanar da gasar a a birnin Zazzau bayan kwashe fiye da shekara 12 ba tare da gudanar da ita ba. A wannan karon gasar ta yi armashi sosai ganin yadda jama'a sukayi tururuwar zuwa filin sukuwan dawaki da turawan mulkin mulka suka gina fiye da shekara 100, domin gane wa idonsu yadda za ta kaya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............
-
Sharhi kan wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai da PSG ta lashe
02/06/2025 Duration: 10minShirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon ya yi duba ne kan wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai da aka yi a ƙarshen mako tsakanin PSG ta Faransa da kuma Inter Milan, inda PSG ta samu nasarar lashe gasar bayan da ta zazzaga wa Inter Milan ƙwallaye biyar. Wannan ne dai karon farko da PSG ta lashe wannan kofi, kuma karo na farko da wata ƙungiya daga Faransa ta lashe shi tun bayan Marseille a shekarar 1993.Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Khamis Saleh............
-
Yadda bukin wasanni na ƙasa ke gudana a Abeokutan Najeriya
26/05/2025 Duration: 10minShirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon tare da Khamis Saleh yi yi dubi ne kan bikin wasannin na ƙasa da ke gudana a jihar Ogun da ke Najeriya.