Wasanni

Mahangar masana game da yadda Dembele ya lashe kyautar Ballon d'Or a bana

Informações:

Synopsis

Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali kan yadda ɗan wasan gaba na PSG ɗan Faransa Ousmane Dembele ya lashe kyautar Ballon d'Or a bana, bayan nasarar shi ta lashe kofuna da dama cikin kakar da ta gabata da ƙungiyar tasa da ke birnin Paris. Duk da cewa anjima ana hasashen Dembele ya lashe wannan kyauta lura da namijin ƙoƙarinsa a kakar da ta gabata, amma wasu na da ra'ayin cewa sam ɗan wasan bai cancanci wannan kyauta ba. Game da wannan saɓanin ra'ayi, shirin na Duniyar Wasanni ya tattauna da masana a fagen na wasanni waɗanda suka bayyana ra'ayoyinsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.