Wasanni

Gudummawar da cibiyoyin horar da matasa ke baiwa ƙwallon Ƙafa a Najeriya

Informações:

Synopsis

Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan lokaci za yi duba ne kan irin gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon Ƙafa ke bayarwa wajen zakulo matasan ƴan wasa da horar da su a Najeriya. A wani bangare na gudummawarsu ga ci gaban wasan kwallon kafa a Nigeria, ɗai-ɗaikun jama’a da ƴan kasuwa kai harma da tsofin ƴan wasan tawagar Super Eagles ta ƙasar, sun fara kafa cibiyoyi masu zaman kan su, da su ke zakulowa tare da horar da matasa don yin fice a harkar ta kwallon ƙafa. Irin wadannan cibiyoyin horar da matasa wasan na kwallon kafa da a turance ake kira FOOTBALL ACADEMY, kan shiga birane da karkara don tuntubar ƙanana da matsakaitan club-club, domin samun ƴan wasan daga wajen su da za a yi rijistarsu a wannan cibiya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..