Bakonmu A Yau
Kan dalilan da ke sanya ƴan Najeriya faɗawa hannun ƴan damfara ta hanyar kuɗaɗen internet
- Author: Vários
- Narrator: Vários
- Publisher: Podcast
- Duration: 0:03:28
- More information
Informações:
Synopsis
Dubban ‘yan Najeriya ne a cikin makon nan suka shiga cikin tashin hankali, sakamakon hasarar sama da Naira Tiriliyan 1 da suka tafka, a dalilin rushewar shafin CBEX, wanda ke hada-hadar kuɗaɗen Intanet. Shafin, ya ja hankalin mutane ne ta hanyar yi musu alƙawarin kason ribar 100 bisa 100 akan dukkanin adadin kuɗin da suka sanya cikinsa da zarar an cika kwanaki 30. Sai dai bayan ɗaukar wani ɗan lokaci, shafin tare da wakilansa da ke Najeriya suka yi layar zana.Kan wannan lamari, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Sagir Muhd mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwararru kan na’ura mai ƙwaƙwalwa ta Najeriya......Danna alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar