Synopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodes
-
Malam Bashir Ibrahim Idris kan cika shekaru 18 da kafuwar RFI Hausa
21/05/2025 Duration: 03minA yau 21 ga watan Mayun 2025, shekaru 18 kenan da Radio France International ya fara yaɗa shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa, wanda kuma shi ne harshen na farko daga Afirka da RFI ta fara yaɗa shirye-shiryenta da shi. Malam Bashir Ibrahim Idris, shi ne Babban Editan RFI Hausa, ya yi muna ƙarin bayani a game da yadda rediyon ya fara da kuma irin ci gaba da ya samu a waɗannan shekaru. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawar da Ƙaribullah Abdulmajid Namadobi ya yi da shi...........
-
Gamatie Mahamadou Yansanbou-Kan ta'addancin masu ikirarin jihadi kan ayarin motocin dakon kaya
20/05/2025 Duration: 03minAƙalla Direbobin manyan motoci uku sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani saban harin da ƴanta’adda masu ikrarin jihadi suka kai kan ayarin motocinsu akan hanyar Burkina Faso zuwa Jamhuriyar a rana lahadin da ta gabata. Wanan ne karo na biyu cikin kasa da shekaru guda da ƴan bindigar ke farwa wadanan motoci tare da banka musu wuta.A kan wanan abokin aiki Oumar Sani ya tattauna da Gamatie Mahamadou Yansanbou, magatakarda kungiyar direbobin manyan motoci UTTAN a Jamhuriya Nijar ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.Danna alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar.
-
Abdullahi Jalo akan ƙorafin arewa a game da jarabawar JAMB
19/05/2025 Duration: 03minDa aalam dai har yanzu da sauran rina a kaba ga hukkumar JAMB, mai shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya a game da matsalar da aka samu a lokacin jarabawar wannan shekarar sakamakon ƙorafin da wasu jihohin arewacin ƙasar ke yi akan ware wasu jihohi huɗu na kudu da hukumar ta yi don sake zana jarawabar. Tuni dai wasu suka yi barazanar zuwa kotu tare da kira ga gwamnati da ta saka baki a lamarin. Kan haka ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barrister Abdullahi Jalo, masanin doka.
-
Farfesa Sheriff Almuhajir kan makomar yankin Tafkin Chadi a ɓangaren tsaro
16/05/2025 Duration: 03minBabban Hafsan tsaron Najeriya, Laftanar Janar Christopher Musa ya ce baya ga amfani da makamai wajen tinkarar mayakan Boko Haram, farfado da Tafkin Chadi zai taimaka wajen samarwa jama'ar yankin sana'oi. Wannan ya biyo bayan ziyarar aikin da ya kai Maiduguri bayan kazaman hare haren da boko haram ta kai cibiyoyin soji.Dangane da wannan bukatar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wani mutumin yankin, Farfesa Sheriff Muhammad Almuhajir.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Umar Saleh Gwani kan faɗuwar jarabawar JAMB a Najeriya
15/05/2025 Duration: 03minHukumar kula da jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya ta JAMB ta nemi gafarar jama'ar kasar saboda matsalolin da aka samu wajen jarabaswar bana, wadda ta kai ga dalibai sama da miliyan guda da rabi suka kasa samun makin da ake bukata. Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede cikin hawaye ya nemi gafarar jama'a da kuma daukar alhakin lamarin.Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Umar Saleh Gwani masanin harkar sadarwa.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Farfesa Khalifa Dikwa kan karuwar hare-haren Boko Haram a Borno
14/05/2025 Duration: 03minYayinda hare-haren ƙungiyar Boko Haram tsagin ISWAP ke ƙara tsananta musamman a Najeriya, rahotanni na cewa mayakan sun shafe ƙarshen makon jiya zuwa Litinin da ta gabata suna kadammar da hare-hare a sassa na jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.A tattaunawarsa da Rukayya Abba Kabara, Farfesa Khalifa Dikwa masanin tsaro a Najeriya ya ce ba abin mamaki bane yadda ‘yan ta’addar suka sauya salon kai hare-harensu. Shiga alamar sauti domin sauraron cikaken bayani.....
-
Dakta Garko akan ƙaruwar masu matsalar ƙwaƙalwa a Najeriya
13/05/2025 Duration: 03minWasu rahotanni a Najeriya na bayani akan karuwar samun mutanen dake fama da rashin lafiyar dake da nasaba da kwakwalwa, sakamakon yanayin rayuwar yau da kullum. Domin sanin tasirin matsalar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Farfesa Bello Bada kan matsalar tsaro a Arewacin Najeriya
12/05/2025 Duration: 03minGwamnonin Arewacin Najeriya tare da Sarakunan yankin sun gudanar da wani taro na musamman domin sake duba matsalolin tsaron da suka addabi yankin, a dai-dai lokacin da mayaƙan Boko Haram da ƴanbindiga ke ci gaba da hallaka jama'a ba tare da ƙaƙƙautawa ba. Bayan kammala taron, Bashir Ibrahim Idris ya tintibi Farfesa Bello Bada na Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto. Kula latsa alamar sauti don sauraron yadda zantawarsu ta gudana akai...........
-
Dr Kassim Kurfi kan dalilan da suke sanya 'yan Najeriya ƙara talaucewa
09/05/2025 Duration: 03minDalilan da suka sanya 'yan Najeriya ke ƙara faɗawa cikin mawuyacin hali sanadiyyar talaucin da ya yi musu katutu. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziƙi a Najeriya Dr Kassim Garba Kurfi.Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawar...
-
Sanata Ali Ndume kan taron da majalisar dokokin ECOWAS tayi a Lome
08/05/2025 Duration: 03minMajalisar dokokin ƙungiyar ƙasashen ECOWAS ta gudanar da taron ta a Lome da ke ƙasar Togo, wanda ya mayar da hankali kan tsadar sufurin jiragen sama a yankin. Bayan taron, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sanata Ali Muhammed Ndume, daya daga cikin shugabannin taron. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar tattaunawar tasu.............
-
Archbishop Kaigama akan yadda ake zaɓen Fafaroma a dariƙar Katolika
07/05/2025 Duration: 03minYau manyan limaman dariƙar Katolika na duniya sama da 130 ke fara gudanar da zaɓen Fafaroma domin maye gurbin Francis da ya rasu a makon jiya.Domin sanin yadda ake gudanar da zaɓen, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Archpishop Ignatius Kaigama, daya daga cikin manyan limaman Katolika a Najeriya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana akai. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....
-
Babu sojan da zai yi ritaya a wannan shekarar a Jamhuriyar Nijar
06/05/2025 Duration: 03minGwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta bai wa hafsan sojojin ƙasar umarnin cewar babu wanda zai tafi ritaya a cikin wannan shekarar, sakamakon wasu matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta. Dangane da wannan umarni, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Sani Yahya Janjuna, mai sharhi akan lamuran yau da kullum, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana akai.
-
Tattaunawa da Hon Samaila Muhammed kan barazanar Meta na ficewa daga Najeriya
05/05/2025 Duration: 03minKatafaren kamfanin sadarwar Meta da ya mallaki Facebook da WhatsApp ya yi barazamar ficewa daga Najeriya, saboda cin tararsa da hukumomin ƙasar suka yi na Dala miliyan 290, sakamako karya ƙa’idodin aikinsa. Najeriya ta samu kamfanin ne da laifin talla ba bisa ƙa’ida ba, da kuma rashin alkince bayanan asiri na jama’ar dake hulɗa da shi.Dangane da wannan dambarwa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hon Samaila Muhammed, masanin tallalin arziki da kuma sadarwa, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana akai.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar
-
Dr. Harbau: Yadda ma'aikata za su nema wa kansu mafita
01/05/2025 Duration: 03minYau ɗaya ga watan Mayu take ranar Ma’aikata ta Duniya, ranar da ake duba gudummawa da sadaukarwar ma’aikata ga al’umma. A kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Dokta Aminu Idris Harbau, masanin tattalin arziki a jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke jihar Kano a Najeriya, wanda ya duba yadda wannan rana ta riski ma’aikata, tare da shawartar su a kan nema wa kansu mafita a yanayi da albashi ba zai wadata ba wajen tafiyar da rayuwa mai inganci.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakakkiyar hirarsu
-
Morocco ta baiwa ƙasashen AES damar yin amfani da tashar ruwanta
30/04/2025 Duration: 03minA daidai lokacin da rikici tsakanin Mali da Algeria ke cigaba da ruruwa, Sarkin Morocco Mohammed VI ya gayyaci ministocin harkokin wajen ƙasashen Burkina Faso,Mali da kuma jamhuriya Nijar a fadarsa da ke birnin Rabat domin basu damar yin fanin da tashar ruwanta na Atlantic wajan jigilar kayakinsu.Ziyarar tasu dai na zuwa ne bayan da alaƙa tsakanin ƙasashen AES da Algeria, wacce ke zama babbar abokiyar hamayyar Morocco ta yi tsami. Latsa alamar sauti domin suraron karin bayani.....
-
Tattaunawa da Farfesa Tukur Abdulkadir kan cikar Trump kwanaki 100 a mulki
29/04/2025 Duration: 03minYau shugaban Amurka Donald Trump le cika kwanaki 100 a karagar mulkin ƙasar, tun bayan rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairun shekarar nan. A tsawon wannan lokaci, shugaban na Amurka ya ɗauki mabanbantan matakai da suak girgiza sassan duniya.Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Tukur Abdulkadir na Jami'ar Kaduna, don jin yadda masana ke kallon salon kamun ludayin Donald Trump ga kuma tattaunawarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar..
-
Malam Isa Sanusi kan kisan fararen hula a jihar Zamfara
28/04/2025 Duration: 03minKungiyar Amnesty International ta tabbatar da mutuwar mutane 26 sakamakon harin ƴan bindiga a wurin hakar zinaren da ke jihar Zamfara. Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Malam Isa Sanusi ne ya tabbatar da haka a tatatunawar da suka yi da Bashir Ibrahim Idris. Ku latsa alamar sautin don sauraron cikakkiyar tattaunawar tasu...........
-
Dalilin da ya sa ƴan adawar Najeriya ke sauya sheƙa zuwa APC
25/04/2025 Duration: 03min‘Yan adawa a Najeriya sun zargi gwamnatin ƙasar ta jam’iyyar APC da yi musu rinto ta hanyar amfani da ƙarfin tattalin arziƙin ƙasa da ke hannunta da kuma wasu dabaru wajen sanya jiga-jigai daga ɓangaren su ‘yan adawar sauya sheka zuwa ga jam’iyya mai mulki. Wannan lamari ya maido da muhawara a tsakanin ‘yan Najeriya a kan dalilan da suke haddasa yawaitar sauyin shekar ‘yan siyasa daga ɓangaren adawa zuwa gwamnati.Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Farfesa Kamilu Sani Fagge na jami’ar Bayero a Najeriya.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyarsu
-
Farfesa Sadiq: Sabon nau'in cutar Polio ya karaɗe wasu jihohin Najeriya
24/04/2025 Duration: 03minAsusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce an samu ɓullar sabon nau’in cutar Polio a ƙananan hukumomi 18 da ke wasu jihohin Najeriya 9 ciki har da Kano. Rahoton ya ce zuwa yanzu an samu rahotanni daban daban aƙalla 18 kan ɓullar sabon nau’in cutar ta Shan Inna, kuma an tattara bayanan ne a cikin watanni uku da suka gabata zuwa yanzu.Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Farfesa Sadiq Isa Abubakar, shugaban cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa na asibitin Malam Aminu Kano da kuma jami'ar Bayero.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu
-
Wasu yankunan Zamfara ba sa samun sauƙi duk da biyan 'yan bindiga da suke yi
23/04/2025 Duration: 03minMazauna ƙauyuka da dama a wasu yankunan jihar Zamfara, ciki har da yankin Gusau ta Gabas, na rayuwa cikin tsananin fargabar fuskantar hare-haren ‘yan bindiga, muddin suka gaza biyan miliyoyin Nairar da ‘yan ta’addan ke tilasta musu bayar wa a matsayin musayar barinsu su zauna lafiya.Yayin ƙarin bayani a kan halin da suke ciki, da kuma ƙauyukan da ke cikin tashin hankalin, wani mazaunin ɗaya daga cikin yankunan, ya ce biyan maƙudan kuɗaɗen da suke yi ba ya kawar da barazanar da suke ciki.