Synopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodes
-
Tattaunawa da Dr Abbati Bako game da buƙatar sauya lokacin zaɓe a Najeriya
15/10/2025 Duration: 03minKwamitin Majalisun Najeriya da ke yiwa kundin tsarin mulki gyaran fuska ya bada shawarar sake dokar zaɓe ta yadda za a dinga gudanar da zaɓuɓɓuka a watan Nuwamba domin bada damar kammala shari'u kafin lokacin rantsar da waɗanda suka samu nasara. Domin sanin tasirin wannan shiri, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abbati Baƙo mai sharhin kan harkokin siyasa ga kuma yadda tattaunawarsu ta kasance. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar....
-
Farfesa Haruna Jibril kan dalilan da suka tilasta ASUU tsunduma yajin aiki
14/10/2025 Duration: 03minMalaman Jami'o'in Najeriya sun kare matakin ƙungiyarsu na tsunduma yajin aikin gargaɗi na makwanni 2, inda suka zargi gwamnati da yaradara. Wannan kuwa na zuwa ne duk da gargaɗin da gwamnatin ƙasar ta yi na amfani da dokar nan ta babu aiki babu biya duk malamin da ya shiga yajin aiki na ASUU. Shugaban ƙungiyar Malaman reshen Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Farfesa Haruna Jibril ya yiwa Bashir Ibrahim Idris ƙarin bayani a tattaunawar da suka yi kamar haka... Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....
-
Malam Ibrahim Garba Wala game da afuwar Tunubu ga wasu Fursunoni
13/10/2025 Duration: 03minƳan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyi dangane da wasu daga cikin mutanen da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yiwa afuwa a makon jiya, inda suke bayyana rashin dacewar afuwar da akan wasu waɗanda suka aikata manya laifuka. Daga cikin waɗanda ake muhawara a kan su akwai masu kisan kai da masu safarar ƙwayoyi da kuma masu safarar makamai. Domin tattauna wannan batu Bashir Ibrahim Idris, ya zanta da Ibrahim Garba Wala, guda cikin masu fafutukar kare haƙƙin Bil'Adama a Najeriya.......... Latsa alamar sauti domin sauraron zantawarsu................
-
Tsohon Jakadan Kamaru a Faransa Ambasada Muhd kan zaɓen ƙasar ta Afrika
10/10/2025 Duration: 03minA ƙarshen wannan mako ne jama'ar ƙasar Kamaru za su kaɗa kuri'a a zaɓen shugaban ƙasa, inda ƴan takara 10 ke neman shugabanci, cikin su harda shugaba Paul Biya dake neman wa'adi na 8. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Jakadan Kamaru a Faransa, Ambasada Muhammad Sani game da zaɓen. Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawarsu...