Synopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodes
-
Matsalolin tattalin arziki sun ka kawo ƙarshen matsayin matsakaitan mutane a Najeriya - Bincike
07/08/2025 Duration: 03minMatsalolin tattalin arziki a Najeriya ya taimaka wajen watsi da matsayin matsakaitan mutane da ke tsakanin al'umma, inda yanzu ake da attajirai ko matalauta kawai. Masanan na gabatar da dalilai daban daban da suka yi sanadiyar samun wannan matsala, wadda ta haifar da wagegen gibi a tsakanin al'umma. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Bashir Ibrahim Idris da Dr Abbati Bako.......
-
Dakta Shu'aibu Shinkafi kan tsanantar hare-haren 'yan bindiga a Zamfara
06/08/2025 Duration: 03min'Yan asalin jihar Zamfara da ke Najeriya, na ci gaba da bayyana matuƙar damuwarsu dangane da ƙaruwar hare-hare da kisan jama'a da 'yan bindiga ke yi. Mazauna wannan jiha da ke Arewa maso Yammacin ƙasar, sun buƙaci haɗin kai tsakanin gwamnatin jihar da ta Tarayya da zumar samar musu mafita ta dindindin. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Sulaiman Shu'aibu Shinkafi daga jihar. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Dakta Auwal Aliyu kan zanga-zangar tsaffin sojojin Najeriya
05/08/2025 Duration: 03minWani adadi da dama na tsaffin sojojin Najeriya da suka ajiye aiki bisa raɗin kansu, sun mamaye gaban ginin Ma’aikatar Kudin ƙasar, inda suka gudanar da zanga-zanga kan rashin biyansu wani kason kuɗaɗensu na Fansho. Zanga-zangar ta safiyar jiya Litinin, na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan makamanciyarta da tsaffin jami’an ‘Yansanda suka yi kan haƙƙoƙinsu. Domin gano bakin zaren warware matsalar tsaffin jami’an tsaron Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Auwal Aliyu Abdullahi, mai magana da yawun Kwamitin musamman da ke kula da walwalar tsaffin sojoji a Najeriya. Shiga alamar sauti domin sauraron ckakkiyar tattaunawar.
-
Dakta Isa Sanusu kan kin hukunta ƴansanda da suka murƙushe zanga-zangar yunwa
04/08/2025 Duration: 03minƘungiyar kare hakkin bil’adama ta Human rights watch ta koka kan yadda har yanzu gwamnatin Najeriya ta gaza ɗaukar mataki kan ƴan sandan da aka zarga da kisan mutane lokacin zanga-zangar yunwa da ta faru a ƙasar a bara. Baya ga haka kuma ƙungiyar ta ce lokaci yayi da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yiwa iyalan ɗan gwagwarmayar nan Abubakar Dadiyata bayanin halin da yake ciki shekaru 6 bayan ɓatansa Shiga alamar sauti don sauraron cikakken bayani....
-
Tattaunawa da Barista Abdullahi Jalo kan taron jagororin Arewacin Najeriya
31/07/2025 Duration: 03minJagororin yankin Arewacin Najeriya sun kammala taron yini biyu da duka gudanar a Kaduna, don bibiyar alkawurran da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ɗaukar wa yankin a lokacin yaƙin neman zabe. Wannan dai na zuwa ne bayan da wasu suka yi zargin cewa an maida yankin saniyar ware duk kuwa da irin gudunmuwar da ya bayar a lokacin zaɓen baya. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Khamis Saleh da Barista Abdullahi Jalo...........
-
A Najeriya duk da zambaɗawa wutar lantarki kuɗi har yanzu ba ta sauya zani ba
30/07/2025 Duration: 01minA Najeriya, duk yadda mahukunta ke tsawwala kudin wutar lantarki, tare da bijirowa da dokokin da suke ganin za su inganta bangaren samar da wutar, har yanzu dai da sauran rina a kaba a game da ƙarancin wutar. Akan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da ɗan gwagwarmaya a jihar Kanon Najeriya, Kwamared Belllo Basi, ga kuma tattaunawarsu.
-
Hira da Sani Roufa'i kan cika shekaru biyu da yin juyin mulki a jamhuriya Nijar
28/07/2025 Duration: 03minRanar 26 ga watan yuli ne aka cika shekaru biyu da kifar da gwamnatin Bazoum Mohamed a Nijar, albarkacin wannan rana shugaban ƙasar Abdurahmane Tchiani ya gabatar da jawabi inda ya bayyana halin da kasar ke ciki. Ra'ayoyi jama'a dai sun sha bamban a kan tafiyar ƙasar a yanzu. Shiga alamar sauti domin jin cikakkiyar hira da Ibrahim Tchillo ya yi da Sani Roufa'i masanin halayya zamantakewa a jamhuriya Nijar....
-
Dr Abdulƙadir Suleiman kan dalilan da ya sanya duniya ta mance da yaƙin Sudan
25/07/2025 Duration: 03minSama da shekaru biyu bayan ɓarkewar yakin basasar ƙasar Sudan, kasashen duniya sun kau da kan su, yayin da ake ci gaba da hallaka fararen hula. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulkadir Suleiman Muhammad, a kan dalilin da ya haifar da yaƙin da kuma yadda ƙasashen duniya suka juyawa ƙasar baya. Latsa alamar sauti domin sauraren hirar...
-
Farfesa Abba Gambo kan barazanar yunwa da mutane sama da miliyan 3 ke fuskanta
23/07/2025 Duration: 03minƘungiyar agaji ta ICRC ta bayyana cewar akwai yiwuwar fuskantar matsalar yunwa a arewa maso gabashin Najeriya sakamakon tashin hankalin da ya tilastawa manoma ƙauracewa gonakin su. Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawar Bashir Ibrahim Idris da Farfesa Abba Gambo...
-
Abubakar Abdullahi mai ritaya kan zanga-zangar tsoffin 'yan sandan Najeriya
22/07/2025 Duration: 03minA ranar Litinin ne tsofaffin 'Yan Sandan Najeriya da suka yi ritaya suka gudanar da zanga-zanga a biranen ƙasar da kuma Abuja, saboda gabatar da ƙorafi akan yadda ake biyan su fansho da kuma neman fitar da su daga tsarin da ake amfani da shi yanzu haka. Bayan kammala zanga zangar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da CSP Abubakar Abdullahi dashe mai ritaya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
An ɗauki hanyar samun zaman lafiya a Jamhuriyar dimokaraɗiyar Congo
21/07/2025 Duration: 03minAn fara samun haske a game da kawo ƙarshen rikicin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, inda a ranar Asabar makon da ya gabata a birnin Doha na Qatar ƙasar, da kungiyar yan tawayen M23 suka rattaba hannu akan wata yarjejeniyar tsagaita wuta da zumar kawo ƙarshen yakin da suke yi a tsakaninsu. A cikin yarjejeniyar, dukkannin bangarorin sun amince su tsagaita kai wa juna hare-hare tare da dakatar da farfagandar nuna ƙiyayya. Akan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Dokta Abbati Bako, masanin dangantakar ƙasa da ƙasa daga jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya.
-
Hira da Kwamared Umar Hamisu Ƙofar Na’isa kan matakin ladabtar da yansanda
17/07/2025 Duration: 03minKamar yadda akaji a farkon Shirin, Hukumar kula da ƴansanda a Najeriya ta gurfanar da manyan jami’ai sama da 150 a gaban kwamitin ladabtarwa, bisa zarginsu da wulakanta aikin ɗansanda da kuma take hakkoki fararen hula a wasu lokutan. Bayanai sun ce an baiwa kwamitin kwanaki 10 ya gama binciken ƴansanda masu muƙamin ASP zuwa sama, ya kuma gabatar da rahoto wanda zai baiwa hukumomi damar ɗaukar matakin hukunci a kansu. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiya hirar.....
-
Tattaunawa da Isma'ila Muhammed ɗan siyasa a Kamaru game da takarar Paul Biya
15/07/2025 Duration: 03minShugaba Paul Biya na Kamaru mai shekaru 92 ya bayyana aniyar sake tsayawa takara don neman wa'adi na 8 na mulkin ƙasar da nufin ci gaba da yiwa ƙasar hidima. Shugaba Biya ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta. Sai dai ko yaya jama'ar Kamaru ke kallon wannan mataki, dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Isma'ila Muhammed ɗan siyasa a ƙasar ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar..
-
Tattaunawa da makusancin Buhari, Faruk Adamu Aliyu kan rasuwar tsohon shugaban
14/07/2025 Duration: 02minA jiya Lahadi, 13 ga watan Yulin nan ne Allah ya yi wa tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari rasuwa yana da shekaru 82 a duniya. Bayan kasancewa shugaban gwamnatin sojin Najeriya daga shekarar 1983 zuwa da 1985, ya sake dawowa a matsayin farar hula, inda ya mulki ƙasar daga shekarar 2015 zuwa 2023. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Faruk Adamu Aliyu, ɗaya daga cikin makusantan Buhari akan wannan rasuwa da irin rayuwar da yayi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....
-
Tattaunawa da Alhaji Garba Suleiman Krako Madakin Saminaka kan ambaliyar Texas
10/07/2025 Duration: 03minRahotanni daga Amurka na cewa an samu ƙaruwar yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon Iftila’in Ambaliyar ruwan da ya afka wa Jihar Texas, inda zuwa yanzu adadin ya haura mutane 115, yayin da har aynzu aka gaza gano wasu aƙalla 160 da suka ɓace. Domin jin halin da ake ciki da kuma dalillan da suka haddasa aukuwar ambaliyar a Texas, Nura Ado Suleiman ya tattauna da mazaunin ƙasar ta Amurka, Alhaji Garba Suleiman Krako Madakin Saminaka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....
-
Tattaunawa da Dr Idris Harbau kan taron ƙasashen BRICS a Brazil
09/07/2025 Duration: 03minA ranar Litinin ƙasashe manbobin ƙungiyar BRICS suka kammala taronsu na 17 a Brazil, inda a cikin kwanaki biyu da suka shafe suna ganawa, jagororin ƙasashen suka tattauna a kan yadda manufofin shugaba Trump ke tasiri kan tattalin arziƙi da kasuwancin Duniya. Sai dai tun kafin kammala taron, shugaba Trump ɗin ya yi barazanar lafta harajin kashi 10 kan kayayyakin ƙasashen na BRICS, da ma duk wata ƙasa da ta goyi bayan matakan adawa da manufofin Amurka. Kan wannan batu, da kuma tasirin ƙungiyar ta BRICS Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Aminu Idris Harbau, masanin tattalin arziƙi da ke Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar..
-
Tattaunawa da Sakataren ƙungiyar direbobin sufuri ta NURTW kan yawaitar haɗurra
08/07/2025 Duration: 03minRahotanni daga Najeriya sun ce mutane da dama ne suka rasa rayukansu sakamakon haɗurran motoci da aka samu a ƙarshen mako cikin jihohin Kano da Jigawa da Bauchi da Lagos da kuma jihar Oyo baya ga Lagos da kuma jihar Kogi. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin hanyoyin motoci ke ci gaba da taɓarɓarewa, yayinda wasu direbobin ke tuƙi cikin yanayi na maye ko kuma saɓawa dokokin tuƙi. Dangane da wannan matsala da ke kaiwa ga asarar ɗimbin rayuka, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Adamu Idris Abdullahi Sakataren ƙungiyar direbobin sufuri ta NURTW da ke Abuja ga kuma yadda tattaunawarsu ta kasance. Sai ku latsa alamar sauti don saurare.
-
Tattaunawa da Honourable Siraj Imam Ibrahim kan ambaliyar ruwan Kano
07/07/2025 Duration: 03minA ƙarshen makon da ya gabata aka samu ambaliyar ruwan sama a sassan birnin Kano, a dai dai lokacin da damina ta fara kankama a jihar. Wannan matsalar ta haifar da matsaloli ga mazauna da kuma baƙin da ke zuwa birnin. Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban ƙaramar hukumar Dala, Hon Siraj Ibrahim Imam, Kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti son sauraron cikakkiyar Hirar.
-
Dr Aliyu Bello kan ƙawancen 'yan adawa a Najeriya
04/07/2025 Duration: 03minA wannan mako ne yan adawan Najeriya suka kafa wani kawancen da suka ce zai tinkari Jam'iyyar APC a zabe mai zuwa, da zummar kawar da ita daga karagar mulki. Shirin Duniyarmu Ayau na RFI Hausa ya gudanar da mahawara tsakanin Sanata Ahmed Babba Kaita na sabuwar kawancen da kuma shugaban Jam'iyyar APC a Jihar Nasarawa Dr Aliyu Bello. Ga kadan daga cikin abinda shugaban APC ya fadi a cikin shirin da zai zo muku gobe da misalin karfe 5 na yamma.
-
Emmanuel Shehu kan haɗakar jam'iyyun adawa a Najeriya da nufin tunkarar APC mai mulki
03/07/2025 Duration: 03minWasu daga cikin jiga-jigan ƴan adawar Najeriya sun haɗa kansu wajen komawa jam'iyyar ADC domin shirin tunkarar gwamnatin APC mai mulki da suke zargi da rashin iya mulki, Yayin gabatar da sabbin shugabannin, ƴan adawar sun sha alwashin ceto talakan Najeriya daga halin ƙuncin da ya samu kansa. Sai dai wasu na cewa neman mulki ne kawai suke yi amma ba don talakan Najeriya ba. Bashir Ibrahim Idris ya tattauwa da shugaban cibiyar horar da ƴan Jaridu ta IIJ da ke Abuja, Dr Emman Shehu, kuma ga yadda zatawarsu ta gudanar.