Bakonmu A Yau
Dakta Auwal Aliyu kan zanga-zangar tsaffin sojojin Najeriya
- Author: Vários
- Narrator: Vários
- Publisher: Podcast
- Duration: 0:03:36
- More information
Informações:
Synopsis
Wani adadi da dama na tsaffin sojojin Najeriya da suka ajiye aiki bisa raɗin kansu, sun mamaye gaban ginin Ma’aikatar Kudin ƙasar, inda suka gudanar da zanga-zanga kan rashin biyansu wani kason kuɗaɗensu na Fansho. Zanga-zangar ta safiyar jiya Litinin, na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan makamanciyarta da tsaffin jami’an ‘Yansanda suka yi kan haƙƙoƙinsu. Domin gano bakin zaren warware matsalar tsaffin jami’an tsaron Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Auwal Aliyu Abdullahi, mai magana da yawun Kwamitin musamman da ke kula da walwalar tsaffin sojoji a Najeriya. Shiga alamar sauti domin sauraron ckakkiyar tattaunawar.