Synopsis
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.
Episodes
-
Gwamnatin Ghana na nazarin yiwuwar fara bayar da ilimin Sakandire kyauta
04/03/2025 Duration: 09minShirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan shirin gwamnatin Ghana na fara bayar da ilimin Sakandire kyauta, kodayake an faro da sauraren ra'ayin jama'a kan wannan shiri wanda ma'aikatar ilimin ƙasar ta bijiro da shi. Bayanai sun ce baya ga bayar da ilimin kyauta, tsarin zai kuma kawo gyara a yanayin bayar da ilimi musamman a manyan makarantun ƙasar ta Ghana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
-
Yadda matasa a Najeriya suka ƙirƙiri injin da ke tsince tsakuwa daga Shinkafa
25/02/2025 Duration: 09minA wannan makon, shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Aisha Shehu Kabara ya mayar da hankali kan yadda wasu matasa suka ƙirƙiri wani nau'in inji da ke cire tsakuwa daga jikin shinkafa, wanda zai taimaka matuƙa wajen samar da tsaftatacciyar shinkafa. Kafin wannan hoɓɓosa daga matasan, akan shigo da irin injinan ne daga ƙasashe irin China don sauƙaƙawa Manoma.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Gwamnatin Najeriya ta ɗaga likafar Kwalejin Kimiyyan Lafiya ta Tsafe zuwa Jami'a
18/02/2025 Duration: 09minShirin “Ilimi Hasken Rayuwa” namu na wannan mako, ya yada zango ne a tarayyar Najeriya, inda shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan ƙudurin samar da sabuwar jami’a kimiyyan lafiya da fasaha ta tarayya wato Federal University of Health Science and Technology a garin Tsafe na Jihar Zamfara, bayan tsallake dukkan matakan majalisa dokokin ƙasar. Wannan saka nannu na shugaban ƙasar ya yi zai bada damar ƙara inganta harkan kiwon lafiya ta hanyar samar da kwararru.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.........
-
Matsin rayuwa na barazanar gurgunta karatun ƙananan yara a Najeriya
11/02/2025 Duration: 09minShirin ''Ilimi Hasken Rayuwa'' tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan yadda halin matsin rayuwa ke yin tasiri a kan karatun yara ƙanana lamarin da ya sa kaso mai yawa daga cikinsu ba sa samun cikakkiyar fahimta a kan darussan da ake koya musu, saboda dalilai da dama masu alaka da matsin rayuwar. Baya ga batun ci a koshi dai, yanyayin da yara ƙanana ke tafiya makarantunsu a yanayin da ake ciki ma lamari ne da ya kamata a mayar da hankali akai, la’akari da cewar a wasu lokutan ɗan hakin da ka raina kan tsone maka ido.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
-
Yadda za'a koya wa yara iya karatu tun daga matakin farko a Najeriya
04/02/2025 Duration: 10minShirin ilimi hasken rayuwa na wannan lokaci ya mayar da hankali kan yadda za'a bi ƙa'idoji da hanyoyi domin koya wa yara iya karatu a matakin farko a Najeriya. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
-
Gasar HIFEST karo na bakwai a Najeriya
28/01/2025 Duration: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, ya yi duba ne, kan yadda wata kungiya a Najeriya, ke karfafa gwiwar daliban sakandire kan yadda za su bayyana baiwar da suke da ita, musamman a bangaren ilimin fasaha.
-
Mahimmancin kwalejojin fasaha a Najeriya wajen bunƙasar ɓangaren ilimin kimiyya
24/12/2024 Duration: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya yi nazari ne kan mahimmancin kwalejojin fasaha na Najeriya ga bunƙasar ɓangaren ilimin kimiyya da fasaha a ƙasar, da kuma kalubalen da suke fuskanta a halin yanzu, sai kuma duba hanyoyin da za a bi don farfaɗo da martabarsu. Ku latsa almar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman............
-
Tasirin da salon koyarwa ke da shi wajen baiwa ɗalibai ingantatcen ilimi
10/12/2024 Duration: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan mako, ya tattauna ne a kan salon koyarwa tun daga matakin makarantu na ƙasa wato ‘Method of Teaching’ a turance, da tasirin da wannan salo ke da shi kan bayar da ilimi. Salo ko kuma dabarun koyarwa matakai ne ko tsarin da malamai ke amfani da su wajen koyar da ɗalibai darussa, a kuma tabbatar da cewa ɗaliban sun fahimci darasin da ake yi musu. A mafi yawan lokuta waɗannan dabaru sukan bambamta a tsakanin darussa, zalika ya danganta da matakan ilimi daga ƙasa, da na tsakiya zuwa na sama.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.......
-
Rashin malamai ya tilasta iyaye janye yaransu daga makarantu a kudancin Najeriya
06/11/2024 Duration: 09minShirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda iyaye a yankin kudancin ƙasar ke janye yaransu daga Makarantu saboda ƙarancin makarantu a yankin. Jihar Abia na sahun ƴan gaba gaba da ke fama da wannan matsala inda a baya-bayan nan aka tarin yaran da suka daina zuwa makaranta.
-
Gwamnatin Bauchi na shirin mayar da yara fiye da miliyan 1 makarantu
29/10/2024 Duration: 09minShirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda gwamnatin jihar Bauchi a Najeriya ke yunƙurin mayar da yara fiye da miliyan guda makaranta a wani yanayi da ake ganin ƙaruwar yaran da basa zuwa makaranta a yankin arewacin kasar. Tuni masu ruwa da tsaki a wannan yanki suka yi maraba da matakin gwamnatin ta Bauchi, lura da yadda yunƙurin zai taimaka matuƙa wajen rage ɗimbin yaran da ke gararamba ba tare da zuwa makaranta ba a Arewacin na Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
-
Ɓanagrorin ilimi sun koka da matakin JAMB na durkusar da harshen Faransanci
24/10/2024 Duration: 10minSannu a hankali darussan nazarin harshen faransanci na kara karbuwa a manyan makarantun Nigeria, sai dai kuma, wani matakin da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB a Nigeria, ta aiwatar, na cire takardar shaidar share fagen shiga jami’a ta karatun harshen faransanci, daga cikin darussan da hukumar ta JAMB ke bayar da guraben karatunsu a manyan makarantu ya daga hankalin masu ruwa da tsaki.
-
Yadda wasu gwamnoni a Najeriya ke biris da yaran talakawa da suka tura karatu wasu kasashe
15/10/2024 Duration: 10minShirin na wannan rana ya duba yadda wasu gwamnonin a Najeriya ke daukar alhakin tura yaran talakawa wasu kasashe domin karatu amma kuma daga bisani sai gwamnatin ta yi biris da sha'aninsu.
-
Yadda jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI
08/10/2024 Duration: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya duba yadda wasu manyan jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin ƙasashen da suka ci gaba kan yadda za a inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI. Tuni kuma suka gabatar da wannan buƙata tasu a wajen taron da ƙungiyar bunkasa ilimi ta ƙasashen Turai kan shirya duk shekara, inda a wannan shekara Faransa ta karbi baƙuncin irin wannan taro da ya samu halartar jami'oi 6 da aka zabo daga Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.......
-
Yadda ake ƙara samun yawaitar masu karatun yaƙi da jahilci a Adamawa
01/10/2024 Duration: 09minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya tattauna ne akan yadda makarantun manya ko kuma na yaƙi da jahilci kamar yadda akan kira su, ke fuskantar ƙalubalen ɗauka ko ilimantar da ɗaliban da yawansu ke ƙaruwa a kullum, adadin da ya zarta na makarantun manyan da ake da su. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara......
-
Hukumar JAMB ta shirya taro kan bai wa naƙasassu dama
24/09/2024 Duration: 10minShirin namu na wannan mako zai yi dubi ne kan yadda hukumar kula da harkar jarabawan shiga jami’o’i a Najeriya wato JAMB da hadin guiwan kungiyar zabiya na kasa ta shirya taron nahiyar Afrika na farko kan baiwa nakasassu ko masu larura ta musamman dangane da harkar ilimi kamar kowani dan adam. Taron an shirya shi ne dai la’akari da irin kalubalen da masu larura ta musamman ke fama da ita a kasashe masu tasowa kamar Najeriya,kama daga kyama,nuna musu banbanci da dai sauransu.
-
Fannin ilimi a Najeriya na fuskantar barazana sakamon matsin tattalin arziki
17/09/2024 Duration: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya yi duba ne a kan yadda matsin tattalin arziki da kuma tsare-tsaren gwamnati suka kassara fannin ilimi a tarayyar Najeriya. Daga ɓangaren mahukunta jami'o'in suna ganin tsare-tsaren da gwamnati ta bullo da su a fannin ilimi sune suka sanya a wannan lokaci ko da gyare-gyare a jami'o'in basa iya aiwatarwa. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara........
-
Har yanzu tsarin jagoranci da bada shawarwari na tasiri a makarantu?
27/08/2024 Duration: 09minShirin a wannan mako ya duba yadda tsarin jagoranci da bada shawarwari a makarantu, tsarin da ke taimakawa dalibai zabar irin fannin da suke son kwarewa akai, inda sun kai matakin jami'a da sauransu. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara
-
Tsarin ilimin Sakandire kyauta a Ghana ya ƙarfafa gwiwar dubban ɗalibai
20/08/2024 Duration: 09minShirin ilimi hasken rayuwa tare da Aisha Shehu Kabara a wannan makon ya mayar da hankali kan tsarin bayar da ilimin Sakandiren kyauta a Ghana, wanda ya taimaka matuka wajen ƙara yawan Ɗaliban da ke halarta karatu a wannan mataki. Duk da cewa shirin ya laƙume kuɗaɗe masu tarin yawa amma gwamnatin ƙasar ta Ghana ta ce ko shakka babu kwalliya ta biya kuɗin sabulu cikin shekaru 5 da fara tsarin.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shiri.
-
Yadda tsarin koyo da koyarwa a karni na 21 ke saukakawa wurin fahimtar karatu
30/07/2024 Duration: 09minA wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan tsarin dabarun koyo da koyarwa a ƙarni na 21 da ake kira da 21st Century Learning Skills a turance.Tsarin dabarun koyo da koyarwa na ƙarni na 21, an soma amfani da shi tun a shekarar 2001 domin zamanantar da tsarin yadda ake koyarwa ta hanyar samar da dabarun zamani da za su taimaka wa malamai wurin fahimtar da ɗalibai, sannan ɗalibai su ma su ji sauƙin fahimtar abin da ake koyar da su a aji. A wannan mako, mun dubi yadda tsarin yake aiki tare yadda ya sauƙaƙa wa malamai da ɗalibai wurin fahimtar karatu a wannan zamani musamman a ƙasashe masu tasowa irin Najeriya.Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
-
Karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana
23/07/2024 Duration: 09minShirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana. Hukumar kididdiga ta kasar GSS ta gano cewa kusan matasa miliyan biyu ne ba sa karatun Boko ko aikin yi ko kuma samun horon sana'o'in dogaro da kai.Ku danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadeer Haladu Kiyawa.