Synopsis
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Episodes
-
Sharhi kan yadda aka kammala wasannin zuwa gasar AFCON da za a yi a Morocco
25/11/2024 Duration: 10minShirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan yadda aka kammala wasannin neman gurbin shiga gasar lashe kofin Afrika. Kuma a tsakiyar makon daya gabata ne aka kammala wasannin neman gurbin zuwa gasar cin kofin AFCON da ke gudana tsakanin ƙasashen Afrika, gasar da Morocco za ta karɓi baƙunci a watan Disamban shekarar 2025. A yanzu dai dukkanin ƙasashe sun san makomarsu kuma ƙasashen 24 da za a ga haskawarsu a gasar ta baɗi sun ƙunshi ita mai masaukin baƙi Morocco da Burkina Faso da Kamaru da Algeria da Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo da Senegal da Masar da Equatorial Guinea da Cote d’Ivoire da Uganda da Afrika ta Kudu da Gabon da Tunisia da Najeriya.Sauran sun ƙunshi Zambia da Mali da Zimbabwe da Tsibirin Comoros da Sudan da Benin da Tanzania da Botswana da kuma Mozambique, a wani yanayi da Bostwana ke samun tikitin gasar karon farko bayan dakon shekaru 12.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh........
-
Gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon ƙafa ke bayarwa a Najeriya
18/11/2024 Duration: 10minShirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan irin gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon ƙafa ke bayarwa wajen zakulo matasan ƴan wasa da horar da su a Nigeria. Wannan dai wani bangare ne na gudummawarsu ga ci gaban wasan kwallon ƙafa a Nigeria, tsofin ƴan wasan tawagar Super Eagles na ƙasar, sun fara kafa cibiyoyi masu zaman kan su, da su ke zakulowa tare da horar da matasa don yin fice a harkar ta kwallon kafa. Irin wadannan cibiyoyin horar da matasa wasan na kwallon kafa da a turance ake kira Football Academy, kan shiga birane da karkara don tuntubar ƙanana da matsakaitan club-club, domin samun ƴan wasan daga wajen su da za a yi rijistarsu a wannan cibiya.Pascal Patrick, tsohon ɗan wasan Super Eagles kuma shugaban Hukumar kwallon kafa ta NFA a jihar Bauchi kana co-odinetan tawagar Super Eagles na Nigeria, na daya daga cikin tsofaffin ƴan wasan ƙasar da suka kafa irin wannan cibiya a jihar Bauchi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......
-
Yadda cece-kuce ya mamaye kyautar Ballon d'Or ta 2024
04/11/2024 Duration: 09minShirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon ya yi dubi ne akan yadda aka gudanar da bikin bada kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2024.
-
Hukuncin da CAF ta yi kan danbarwar Najeriya da Libya da kuma wasan El-Clasico
28/10/2024 Duration: 09minShirin Duniyar Wasanni na wannan makon yayi duba ne kan yadda wasan El-Clasico ya gudana da kuma hukuncin da Hukumar Kwallon Ƙafar Afrika CAF tayi kan danbarwar Najeriya da Libya. A ƙarshen mako ne dai kwamin ladaftarwa na hukumar CAF, ya zartar da hukuncin cewa Najeriya ce tayi nasara da ci 3 da nema kan Libya, tare da tarar dala dubu 50. Haka nan shirin ya duba yadda wasan El-Clasico ya gudana tsakanin Real Madrid da Barcelona da aka yi a ƙarshen mako.
-
Danbarwar da ta ɓarke kan wasa tsakanin Najeriya da Libya
21/10/2024 Duration: 10minShirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan danbarwar da aka samu tsakanin Najeriya da Libya. A makon daya gaba ne dai aka fara kai ruwa rana tsakanin bayan da tawagar Super Eagles ta Najeriya ta yi tattaki zuwa Libya don karawa da takwaransu ta ƙasar a wasa na biyu na neman gurbin zuwa gasar lashe kofin Afrika da za ayi a Morocco a shekara mai zuwa. Wannan al’amari dai ya haifar da cece-kuce a duniyar kwallon ƙafar, ganin yadda Super Eagles ta zargi hukumomin kwallon ƙafar Libya da yin watsi da su a filin jirgin sama ba tare da ance kuci kanku ba.Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....
-
Yadda aka faro kakar gasar Firimiyar Ingila ta bana
14/10/2024 Duration: 09minShirin a wannan makon ya maida hankali ke kan yadda aka faro gasar Firimiyar Ingila, inda akwa yanzu kowace ƙungiya ta samu nasarar buga wasanni 7-7. Tuni gasar ta soma nisa, inda Liverpool take a saman teburi da maki 18, yayinda Arsenal da Manchester City ke biye mata da maki, 17, kowannen su. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
-
Ko komen da Ahmed Musa yayi Kano Pillars zai haifar da ɗa mai ido?
07/10/2024 Duration: 09minShirin Duniyar Wasanni na wannan lokaci yayi duba ne kan komen da Kyaftin din tawagar Najeriya Ahmed Musa ya yi wa tsohon ƙungiyarsa Kano Pillars tare da abokin wasansa Shehu Abdullahi. A karshen makon da muka yi bankwana da shi ne dai ƙungiyar kwallo ƙafa ta Kano Pillars a hukumance ta sanar da kulla yarjejeniyar shekara guda da ƴan wasan. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
-
Matakin da Hukumar CAF ta ɗauka kan Ghana ya bar baya da ƙura
30/09/2024 Duration: 09minA dai-dai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiyen wasannin sharen fagen samun gurbi a gasar lashe kofin Afrika, Hukumar Kula Ƙwallon kafar Afrika CAF ta ce filayen wasan ƙasar Ghana ba su da ingancin da ya kamata a ce an gudanar da manyan wasanni na kasa da kasa a cikin, matakin da ke kara nuna gazawar ƙasar. Ita dai hukumar CAF ta ce ba komai ya sanyata daukar wannan mataki ba, face yadda ta ce aƙwai rashin wadatatciyar ciyawa da rashin magudanun ruwa da dai sauransu a filin wasa na Baba Yara da ke birnin Kumasi, haka ta ce abin ya ke a sauran filayen wasanni irin na Cape Coast da kuma na Accra.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
-
An shiga mako na uku a gasar firmiyar Najeriya
23/09/2024 Duration: 09minShirin a wannan lokaci zai leka gasar Firimirar Najeriya wato NPFL Wanda aka shiga mako na uku da somawa.Gasar Firimiyar Najeriya na daga cikin manyan gasannin Lik-lik da ake ji da su a nahiyar Afrika, musamman idan akayi la’akari da yadda ƙungiyoyin da ke fafatawa a wannan gasa ke taka rawar gani a gasar zakarun Ƙungiyoyin Afrika.
-
Koma bayan da harkokin wasanni ke fuskanta a Najeriya
16/09/2024 Duration: 10minShirin a wannan makon zayyi duba ne kan koma bayan da harkar wasannin ke fuskanta a Najeriya.Najeriya daya ce daga cikin kasashen da suka yi suna a fagen wasanni a duniya, inda ake ganinta a sahun gaba wajen wakiltar nahiyar Afrika.To sai dai a baya-bayan nan kasar na fuskantar koma baya a bangare, musamman idan aka yi la’akari da rashin katabus din da ta yi a lokacin gasar Olympics da aka gudanar a birnin Paris.
-
Yadda aka kammala gasar Paralympics da birnin Paris ya karbi bakunci
09/09/2024 Duration: 09minShirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi duba ne kan yadda aka kammala gasar gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta nakasassu wato Paralympics da birnin Paris ya karbi bakunci, bayan kwashe tsawon kwanaki 11 ƴan wasa dubu 4 da dari 4 su na fafatawa a wasanni 22 da aka lashe lambobin 549. Kasar China ce dai ta jagoranci teburin lashe lambobin yabo na wannan gasa, bayan da ta lashe lambar zinari 94 da azurfa 76 sai kuma tagulla 50, a jumlace tana da lambobin yabo 220. Ku latsa alamar Sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
-
Sauye-sauyen da aka samu a sabuwar gasar zakarun nahiyar Turai
02/09/2024 Duration: 09minShirin a wannan makon zayyi duba ne kan sauye-sauyen da a Ka samu a gasar cin kofin zakarun turai.A makon da ya gabata ne dai hukumar kula wasannin kwallon kafar Turai UEFA ta gudanar da hadin yadda wasanin rukuni na gasar zakarun Turai karo na 70 zai gudana, ganin cewa a wannan karon an samu sauye-saye da dama a gasar. Kadan daga cikin sauye-sauyen da aka samu sun hada da kara yawan kungiyoyin da ke fafatawa a wannan gasa daga 32 zuwa 36.Har illa yau, a wannan sabon tsarin hukumar ta sauya tsarin rukuni da a baya ake amfani da shi, in da a yanzu tazo da tsarin da ke kama da na lik-lik, inda kungiyoyi za su buga wasanni takwas maimakon 6 a matakin farko Kuma dukkanin kungiyoyin zasu kasance a teburi daya, sannan kungiyoyi 8 da suka fi yawan maki ne zasu wuce mataki na 16, wadanda suka kare daga mataki na 9 zuwa na 24 zasu sake neman gurbin ci gaba da zama a gasar sai Kuma daga 25 zuwa na 36 zasu koma gida ma’ana an yi waje rod da su.
-
Yadda ake ci gaba da gasar wasannin motsa jiki na Olymmpics 2024 a Paris
05/08/2024 Duration: 09minWasannin guje-guje da tsalle-tsalle da ke gudana a nan birnin Paris na tafiya yadda aka tsara, inda kawo yanzu an kammala wasu wasanni da dama wasu kuma ana daf da kammala su. 'Yan wasan tawagar kwallon kwando ta Mata ta Najeriya na ci gaba da fatan ganin a wannan karon ta samu nasarar tsallake matakin rukuni, ganin yadda suka dage wajen lashe wasansu na farko da Austrelia amma sai dai sunsha kashi a hannun Faransa a wasa na biyu inda a yanzu fatansu shine samun nasara a wasan da zasu yi da Kanada don tsallakawa matakin dab da na kusa da na karshe a wannan gasa.
-
Shirye-shiryen gudanar da gasar olympics 2024 a Paris sun kammala
22/07/2024 Duration: 09minYau shirin zai yi, duba ne kan yaddata kaya a game da sshirye-shiryen gudanar da gasar olympics da za a fara a cikin wannan watann a birnin Paris. shirye-shirye dai sun yi nisa a game da wannan gasa, duba da cewa ilahirin tawagogin kasashe sama da ɗari 2 da za su fafata a wasanni dabam-dabam sun sauka a wannan birni, haka ma mabobin kwamitin shirya wannan gasa. Wani sabon al'amri kuwa shine yadda za a gudanar da bikin fara wannan gasa a cikin kogin Seine daya ratsa birnin Paris.
-
Yadda El-Kanemi ta lashe kofin ƙalubale na Najeriya na farko cikin shekaru 32
15/07/2024 Duration: 10minShirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali ne kan nasarar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta El-Kanemi Warriors ta lashe kofin kalubale na Najeriya na shekarar 2024. A karshen watan da ya gabata ne dai ƙungiyar ta Jihar Borno ta samu nasarar lashe kofin kalubale na Najeriya, bayan da doke Abia Warriors da ci 2 - 0 a filin wasa na Mobolaji Johnson da ke Lagos.
-
An kammala gasar firimiyar Najeriya ta kakar 2023/2024
08/07/2024 Duration: 10minShirin awannan mako zai maida hankali ne kan gasar Firimiyar Najeriya ta NPFL da aka kamala, ta kakar 2023 2024, gasar da Enugu Rangers ta lashe.To kamar yadda kuka ji tuni kungiyar Enungu Rangers ta lashe gasar Firimiyar Najeriya ta bana da aka kammala, yayin da kungiyar Remo da Enyimba suka kasance a matakin na biyu dana uku To tun bayan kammala gasar masu sharhi ke faman tabka muhawara game da yadda gasar ta gudana, Isma’ila Abba Tangalash mai sharhin ne kan lamuran wasanni, ya mana bayanin yadda gasar ta gudana a dunkule.
-
Yadda sakamakon wasannin gasar kasashen Turai ke ba da mamaki
01/07/2024 Duration: 10minShirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda gasar cin kofin Nahiyar Turai ci gaba gaba da bada mamaki, ganin yadda kananan kasashe ke doke manyan da suka yi suna a bangaren kwallon kafa a duniya. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
-
Tarihin gasar Euro da kuma wainar da ake toya wa a gasar da ke gudana a Jamus
24/06/2024 Duration: 10minShirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda gasar Turai wato Euro 2024 ke gudana a kasar Jamus. gasar Euro, wacce hukumar kula da kwallon kafar Turai ke shiryawa duk bayan shekaru 4. Shirin ya yayi waiwaye kan tarihin ita wannan gasa da kuma irin wainar da ake toyawa a gasar da yanzu haka ke gudana. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
-
Fatanmu wasan Damben gargariya ya shiga wasannin Olympics - Dambe Warriors
10/06/2024 Duration: 10minShirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan ci gaban da wasan Damben Gargajiya ke samu a kasar Hausa. Akwai kungiyoyi da dama da a yanzu suka shiga cikin sabgar wasan dambe wanda kuma hakan ke kara mata tagomashi dama jawo ra’ayin wadanda da basa ciki shiga cikinta gadan-gaban. Dambe Warriors na daga cikin kungiyoyi da ke suka jima suna shirya wasan inda 'yan wasan ke samun albashi mai tsoka a mataki daban-daban. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
-
Mahawara kan yadda kungiyar Madrid ta lashe kofin zakarun Turai
03/06/2024 Duration: 09minShirin Duniyar Wasanni a wannan makon, ya maida hankali ne kan wasan karshe na gasar zakarun Turai wanda kungiyar Real Madrid ta lashe karo na 15 a tarihi, bayan doke Brussia Dortmund, abunda ya maida ita kungiyar data fi kowwacce nasarar dauke wannan kofi mafi girman dearaja a Turai. Gabanin wasan dai ana ganin da wahala Madrid din ta iya samun nasara lura da yadda Dortmund ta zo matakin wasannan na karshe, duk kuwa da cewar tarihin Madrid din na nuna tafi iya lashe kofin data sha wahalar zuwa wasan karshe.Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....